‘Yan Sanda sun kama wadanda ake zargi da garkuwa da Mai ba Gwamna Sule shawara

‘Yan Sanda sun kama wadanda ake zargi da garkuwa da Mai ba Gwamna Sule shawara

Kwanaki baya aka sace wani cikin Hadiman gwamna Abdullahi Sule. Yanzu mun ji cewa Dakarun ‘Yan Sandan Najeriya da ke jihar Nasarawa sun kama wadanda ake zargi da laifin.

Jaridar Daily Trust ta ce ‘Yan Sanda sun kama mutane goma wadanda ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da Mista John Mamman wanda aka samu ya kubuta a Ranar Talatar da ta wuce.

Wadanda su ka sace Mai ba gwamnan na jihar Nasarawa shawara sun bukaci a biya kudin fansar Naira miliyan 20 kafin su sake shi. A halin yanzu garkuwa da mutane ya zama ruwan dare.

Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Nasarawa, Bola Longe ya gabatar da wadanda ake zargi da laifin garkuwa da wannan Bawan Allah. Jami’an tsaro sun gabatar da su ne a babban birnin Lafia.

“An kama wani daga cikinsu sa'ilin da su ka yi garkuwar, inda Dakarun SARS da ke karkashina da Jami’an SIIB da wasu Ma’aikatan musamman su ka matsawa masu garkuwar lambar.”

KU KARANTA: Abin da ya sa na burmawa luwadi Inji 'Dan shekara 58

‘Yan Sanda sun kama wadanda ake zargi da garkuwa da Mai ba Gwamna Sule shawara

Kwanaki aka sace Mai ba Gwamna Sule shawara a kan harkar Masarautu da kananan hukumomi
Source: Twitter

CP Bola Longe ya ce wadanda su ka sace Hadimin na gwamna Abdullahi Sule sun fake ne a bayan wata makarantar sakandaren gwamnati da ke Garin Gudi, a karshe aka yi nasarar cafke su.

Shugaban ‘Yan Sandan na jihar ya shaida cewa Ma’ikatan ‘Yan banga sun taimaka masu wajen kai wa wasu Matasa uku daga cikin wadanda ake zargi da wannan mummunan laifi farmaki.

"A wannan hari ne aka yi caraf da Matasa uku dauke da kudi N1, 163, 500 a kan hanyar Yelwa zuwa Doma. Daya daga cikin wadannan Samari ya tsere, amma biyu su na hannun ‘Yan Sanda."

Bola Longe ya kuma tabbatar da cewa an karbe wani babur kirar Honda a hannun wadanda ake zargin. Wani daga cikinsu wanda aka kama ya ce ya fito ne daga Kauye mai suna Adavi.

Sunan wannan Bawan Allah Usman Shehu, kuma ya na da shekaru 22 a Duniya. Garin Adavi ya na cikin karamar hukumar Doma. An sace Mamman ne a gidansa da ke cikin Garin Kokona.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel