Kwalliya ba ta biya kudin sabulu a tsarin SIP ba – inji Lawan da Gbajabiamilla

Kwalliya ba ta biya kudin sabulu a tsarin SIP ba – inji Lawan da Gbajabiamilla

Shugabannin majalisa, Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila su na ganin gwamnatin tarayya ta gaza sosai wajen dabbaka tsare-tsaren SIP da aka kirkiro domin inganta rayuwar Talaka.

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kashe fiye da Naira Tiriliyan biyu a wannan tsari na SIP daga 2016 zuwa yanzu. Amma shugabannin majalisar su na ganin ba a iya cin ma buri ba.

Shugabannin majalisar dattawa da wakilan sun yi wannan bayani ne a Ranar Talata a lokacin da su ka gana da Ministar bada agaji da tallafin gaggawan Najeriya Hajia Sadiya Umar Farouq.

Sanata Ahmad Ibrahim Lawan da Rt. Hon. Femi Gbajabiamila sun koka a kan cewa kudin da aka warewa wannan tsari ba su kai ga ainihin wadanda aka tanadi tsarin domin su ba a Najeriya.

The Nation ta ce a dalilin haka ne Dr. Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila su ka bukaci Ministar ta sake duba tafiyar wadannan shiri domin ganin wadanda aka tsara abin dominsu su na mora.

Hadimin shugaban majalisar dattawa, Ola Awoniyi, ya fitar da jawabi bayan wannan zama da aka yi a Abuja. Awoniyi ya ce Ovie Omo-Agege da Idris Wase sun halarci wannan taro na jiya.

KU KARANTA: Atiku ya na so Buhari ya rage kudin 'Yan Majalisa saboda annobar COVID-19

Kwalliya ba ta biya kudin sabulu a tsarin SIP ba – inji Lawan da Gbajabiamilla
Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamilla sun ce akwai gyara a shirin SIP
Asali: UGC

Ahmad Lawan ya ke cewa Majalisar tarayya ta damu da wannan shiri da aka kirkira domin rage radadin Marasa karfi, don haka ne ya bukaci a tabbatar wajen ganin Talakawa sun amfana.

Sanatan ya bukaci sabuwar ma’aikatar da ke da alhakin kula da wannan shiri ta yi kokari wajen ganin an waiwayi wadanda talauci ya yi wa kullin goro a wannan lokaci na annobar COVID-19.

“Ina fada maku cewa mafi yawan wadanda za su amfana da wannan tsari ba su da wutar lantarki, ba su san shafin gizo ba. Ba su da asusu a banki, don haka ba su da lambar BVN.” Inji sa.

Lawan ya kara sukar sharudan da aka sa, ya ce: “Kai bari ma, mafi yawansu ba su da wayar salula, wadannan su ne ainihin Talakawa tubus, amma sharudan da aka sa ya ya yi watsi da su.”

Femi Gbajabiamila ya tambayi Ministar: “Ina ku ka samu sunayen Talakawanku, ta ya ku ka yi kason, wani sharadi aka zaba, wani Yanki ku ka dauko” Ya ce akwai bukatar a san wadannan.

Shugaban majalisar wakilan ya bayyana cewa a matsayinsu na Wakilan jama’a dole su san yadda wannan tsari ya ke aiki. A karshe Ministar ta nuna cewa ta ji dadin hadin-kan ‘Yan majalisar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng