An maida Johnson zuwa sashen ICU a asibiti yayin da ya ke fama da COVID-19

An maida Johnson zuwa sashen ICU a asibiti yayin da ya ke fama da COVID-19

A jiya da rana kun ji cewa an tafi da Firayim Ministan Birtaniya, Boris Johnson asibiti domin a samu damar kula da lafiyarsa sosai, inda ya ke fama da cutar COVID-19.

Yanzu haka wani labari maras dadi ya bayyana inda aka ji cewa halin lafiyar Firayim Ministan ya cabe. Wannan lamari ya tada hankalin mutanen Ingila da sauran kasashe.

Mun samu labari daga Sky News cewa an kai Boris Johnson sashen ICU a asibiti inda ake kula da wanda lamarin su ya yi muni. Johnson ya na kwance ne a Garin Landan.

Kakakin gwamnatin Birtaniya wanda ke magana a madadin gidan gwamnati da ke Layin Downing a Landan, ya bayyana cewa Firayim Ministan ya shiga wani hali.

A dalilin haka ne Firayim Minista Boris Johnson ya bada umarnin cewa Ministan harkokin waje watau Dominic Raab ya tsaya masa idan bukatar hakan ta tashi a gwamnatin.

Labarin da ke zuwa daga babban birnin Landan shi ne an kakabawa Johnson na’urar numfashi a bakinsa kafin a tafi da shi zuwa sashen ICU a Ranar Litinin din da yamma.

KU KARANTA: Coronavirus ta buge Firayim Ministan Birtaniya Boris Johnson

Mista Chris Mason wanda ke aiki da sashen BBC ya bayyana cewa a jiya da rana, Firayim Ministan bai kai ga amfani da na’urar ‘Ventilator’ mai taimakawa numfashi ba.

An kwantar da Firayim Ministan mai shekaru 55 a asibiti ne a Ranar Lahadi bayan alamomin Coronavirus sun bayyana a jikinsa, inda ta kai ba za a iya ajiye sa a gida ba.

“Firayim Minista ya na karkashin kulawar Likitocin asibitin St. Thomas a Landan bayan da aka kai shi asibitin sakamakon alamomin cutar COVID-19 da ya ke ta fama da su.”

Jawabin Kakakin gwamnatin ya ce: “Zuwa Litinin da rana, jikin Firayim Ministan ya tabarbare, an kai shi sashen ICU na asibitin bisa shawarar da Likitocinsa su ka bada.”

“Firayim Ministan ya na samun kyakkyawar kulawa, mun godewa Malaman kiwon lafiyan kasar da namijin kokari da jajircewar da su ke yi.” Inji Kakakin gwamnatin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel