Yan bindiga sun kashe mutane 22 sannan suka kona gidaje a Sokoto

Yan bindiga sun kashe mutane 22 sannan suka kona gidaje a Sokoto

Wasu yan bindiga sun kai hari kauyen Gangara a karamar hukumar Sabon Birni da ke jahar Sokoto inda suka kashe mutane 22 da kona kayayyaki da dama.

A cewar wani idon shaida, wasu kauyawa sun jikkata sakamakon harbin bindiga yayinda har yanzu ba a ga wasu ba.

An dauki wadanda suka jikkata zuwa asibitoci mafi kusa domin samun kulawar likita yayinda aka binne wadanda suka mutu a harin kamar yadda addinin Islama ta koyar.

Daya daga cikin shaidun, Laminu Umar, ya bayyana cewa wannan shine karo na farko da ake kaiwa kauyen hari bayan yunkurin kai hare-hare da dama da yan bindigan suka so yi a baya, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Yan bindiga sun kashe mutane 22 sannan suka kona gidaje a Sokoto
Yan bindiga sun kashe mutane 22 sannan suka kona gidaje a Sokoto
Asali: UGC

“Sun yi yunkurin kai mamaya kauyen lokuta da dama amma mazauna kauyen na dakilewa. Muna zargin sun gayyaci abokansu daga sauran jihohi ne don haka suka yi nasara a wannan lokacin,” in ji shi.

“Sun zo da misalin karfe 3:00 na rana kan babura sama da 150, kowani babur na dauke da yan ta’adda uku. Sai suka fara harbi ba kakkautawa, inda suka kashe mutanen da suka gani tare da kona gidaje da ababen hawansu.”

A cewarsa yan ta’addan da suka shafe kusa is sa’a biyu sun kuma sace wasu mutane da dabobbi.

Wani idon shaida da ya nemi a sakaya sunansa ya ce yan bindigan sun gudu jeji bayan sun ga motocin sojoji na tunkarar kauyen.

Kakakin yan sandan jahar Sokoto, DSP Muhammad Sadiq, ya tabbatar da harin sannan ya yi alkawarin karon bayani kan harin bayan ya dawo daga wajen tabbatar da dokar rufe iyakokin jahar da gwamnatin ta yi umurni.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Dakarun rundunonin Sojin kasashen Najeriya, Nijar da Chadi sun kaddamar da wasu sabbin hare hare domin bankado mayakan Boko Haram tare da fatattakarsu daga sabuwar mabuyar da suka koma na tsibirin Tunbuns dake tafkin Chadi.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa yan ta’addan sun tsere zuwa tsibirin sakamakon rakiyan Kura da Sojojin Najeriya suka musu daga inda suka saba kaddamar da hare hare a kan fararen hula mazauna kauyukan yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel