Tattalin arziki: Kudin gangar mai ya yi kasa zuwa $22 a kasuwa

Tattalin arziki: Kudin gangar mai ya yi kasa zuwa $22 a kasuwa

Farashin danyen mai na Brent ya sauko zuwa $22 a kan kudin kowane ganga. Farashin man bai taba yin araha irin haka ba a cikin shekaru kusan 12 da su ka wuce.

Rahotanni sun bayyana cewa a farkon makon nan ne farashin gangar danyan man ya lula kasa haka. Fiye da fam Dala $2.8 ya ragu da farashin gangar man na Brent.

A jiya Litinin da kimanin karfe 5:00 na yamma, ana saida gangar danyen man a kan fam Dala $21.76. A karshen makon jiya an saida gangar danyen man a $22.10.

Reuters ta ce rabon da kudin mai ya sauko kasa haka tun cikin Watan Maris a 2002. A cikin watanni 216 da su ka shude, danyen mai bai taba rasa daraja haka ba.

Wannan karyewa da mai ya yi a cikin ‘yan kwanakin bayan nan ne ya jawo gwamnatin Najeriya ta rage burin abin da za ta samu daga mai a wannan shekara ta 2020.

KU KARANTA: 'Dan Majalisar Najeriya ya roki a dakatar da biyan kudin ruwa da wuta

Tattalin arziki: Kudin gangar mai ya yi kasa zuwa $22 a kasuwa
Karamin Ministan fetur na Najeriya, Sylva Marlin Timipre
Asali: UGC

Da farko gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi lissafin saida kowane gangar danyen mai a kan fam Dala $57. Yanzu dole kasar ta maida lissafinta a kan $30.

Danyen man Brent ya rasa kusan kashi 60% na ainihin farashinsa. A halin yanzu kamfanonin mai sun fara tafka asara, har ta kai wasu sun fara tunanin tashi aiki.

Masu hasashen farashin man su na ganin cewa ba za a taba komawa yadda aka saba yin rububin mai ba, musamman ga kamfanonin jiragen sama da ke sayen man jirgi.

Kasashen OPEC irin su Najeriya. Angola, Aljeriya da Venezuela su na cikin wadanda za su fi girgiza domin ba za su iya takara da Saudi Arabiya da Rasha a kasuwa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng