FCTA ta kama wani Fasto saboda bijirewa dokar tara jama’a a Apo
Wasu Jami’an FCTA da ke aikin tabbatar da doka a babban birnin tarayya Abuja sun kama Faston da ya sabawa ka’ida, ya jagoranci ibada a coci a Ranar Lahadi.
Kamar yadda mu ka samu labari, Jami’an na FCTA sun damke Fasto U. U Uden a sakamakon kin bin doka da ya yi na rufe duk wasu wuraren ibada a Garin Abuja.
Wannan Fasto ya bude cocinsa inda aka yi ibada a Ranar 29 ga Watan Maris. A daidai wannan lokaci an bukaci a rufe coci saboda gudun yaduwar Coronavirus.
A wani bidiyo da ya shiga hannun ‘Yan jarida, an ga yadda Jami’an FCTA su ka hallara cocin nan na ‘Jesus Reigns Family Church’ a Ranar Lahadin da ta gabata.
Rahotanni sun ce Ma’aikatan sun jira Limamin ya gama jagorantar ibadar kafin su cafke shi. Wannan coci ya na cikin Yankin Apo a babban birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA: Osinbajo da Hadimansa sun gagara zuwa coci saboda annobar COVID-19
Mista Ikharo Attah wanda shi ne shugaban wannan Dakaru, ya shaidawa ‘Yan jarida cewa sun kama wannan Fasto bayan da ya kammala huduba ga Mabiyansa.
Ikharo Attah ya ce sun yi wa Faston bayanin yadda ya sabawa doka, bayan haka kuma su ka yi gaba da shi cikin lalama domin ya amsa wannan laifin da ya aikata.
Jami’an sun jira sai da aka kammala ibadar ne sannan su ka kama Limamin cocin domin gudun wani rikici ya barke tsakanin Mabiya da kuma Dakarun na FCTA.
An wuce da Faston zuwa ofishin ‘Yan Sanda da ke Garki inda aka mika shi a hannun Jami’an tsaro. Haka zalika an fatattaki sauran Mabiyan da ke cikin cocin na sa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng