Kano, Kaduna, Maiduguri da sauran manyan biranen da babu cibiyar gwajin kwayar cutar coronavirus

Kano, Kaduna, Maiduguri da sauran manyan biranen da babu cibiyar gwajin kwayar cutar coronavirus

Har yanzu cibiyoyin gwajin kwayar cutar coronavirus da gwamnatn tarayya ta shirya bude wa a Kano, Maiduguri, da Abakaliki basu fara aiki ba duk da kwayar cutar COVID-19 na cigaba da yaduwa a kasa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa ranar Lahadi.

A jiya, Asabar, ne cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta sanar da samun karin wasu mutane takwas da suka kara kamuwa da kwayar cutar COVID-19, lamarin da ya sauya jimillar masu dauke da kwayar cutar zuwa mutum fiye da 90, adadin zai iya karuwa kowanne lokaci, sannan ya nuna cewa an adadin masu dauke da kwayar cutar ya rubanya a cikin kwanaki biyu kacal.

Jihar Legas ce ta fi sauran jihohin Najeriya yawan adadin mutanen da suka kamu da kwayar cutar coronavirus da adadin mutane fiye da 50, sai Abuja a mataki na biyu da adadin mutane 12.

Tuni kwayar cutar coronavirus ta bulla a sassa biyar daga cikin shidda na kasar nan, yankin arewa maso yamma ne kadai ba a taba samun sanarwar wani ya kamu da kwayar cutar COVID-19 ba.

Kano, Kaduna, Maiduguri da sauran manyan biranen da babu cibiyar gwajin kwayar cutar coronavirus
Cibiyar gwajin kwayar cutar coronavirus
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa bincikenta ya nuna mata cewa har ya zuwa safiyar ranar Lahadi, babu cibiyar gwajin kwayar cutar coronavirsu a yankin kudu masa gabas, arewa maso yamma da arewa maso gabas.

DUBA WANNAN: Gwamnoni 5 da suka killace Kansu bayan mu'amala da masu coronavirus

A cikin makon da ya gabata ne ministan lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya sanar da cewa gwamnatin tarayya za ta bude karin wasu cibiyoyin gwajin kwayar cutar COVID-19 a Kano, Maiduguri, da Abakaliki domin rage lodin da ke kan cibiyoyi 5 kacal da ke aiki yanzu.

Cibiyoyin gwajin kwayar cutar coronavirus da ke aiki yanzu a Najeriya sune; na cibiyar NCDC da ke Abuja, asibitin kwararru da ke Irrua a jihar Edo, asibitn koyarwa na jami'ar Legas, cibiyar gwajin cututtuka masu yaduwa da ke Ede a jihar Osun, cibiyar bincike mai zurfi a bangaren lafiya da ke Legas da kuma asibitin cututtuka masu yaduwa da ke Yaba a jihar Legas.

Daily Trust ta bayyana cewa har yanzu sai an yi jigilar jini zuwa Abuja daga Kano domin gudanar da gwajin cutar coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel