Ka da a kyale asibitocin kasuwa su rika gwajin COVID-19 Inji Sani

Ka da a kyale asibitocin kasuwa su rika gwajin COVID-19 Inji Sani

A Ranar Larabar nan ne aka ji Attajirin Afrika, Aliko Dangote ya na kira ga hukumomi su bada dama ga asibitocin kasuwa su rika gudanar da gwajin cutar COVID-19.

Shehu Sani ya yi maza ya fito ya nuna cewa akwai hadari a wannan shawara, tsohon ‘Dan majalisar ya fito ya ce ka da gwamnati ta biyewa wannan kira da aka yi.

Ko da Sanata Shehu Sani bai kama suna ba, kalaman na sa sun nuna inda ya dosa, kuma sun tabbatar da cewa ba ya goyon a ba asibitocin kasuwa damar yin gwajin.

Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019 ya ce asibitocin kasuwa ba za su iya fitowa su fadawa Duniya gaskiyar lamari ba.

“Ka da a kyale asibitocin kasuwa su rika gudanar da gwajin COVID-19. Ba zai taba yiwuwa asibitocinmu na kasuwa su fadi gaskiya da ainihin halin Marasa lafiyansu ba.”

KU KARANTA: Dangote: Gwamnati ta bar sauran asibitoci su rika gwajin COVID-19

A ra’ayin Shehu Sani, ba zai yiwu ace asibitocin da ba na gwamnati ba, su bayyana halin lafiyar wadanda su ka biya kudi domin ayi masu gwajin cutar ta Coronavirus.

Kwamred Sani ya yi wannan bayani ne a shafinsa na Tuwita a Ranar Laraba, 24 ga Watan Maris. Daga baya ya kuma jawo hankalin gwamnatin tarayya game da lamarin.

Shararren ‘Dan siyasar ya bukaci hukumar NCDC mai kula da cututtuka a Najeriya ta saurari wannan shawara da ya fito ya bada a lokacin da kasar ta ke fama da cutar.

Kwanakin baya kuma Shehu Sani ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi amfani da kungiyar CAN da Mai alfarma Sarkin Musulmi wajen yakin da ta ke yi da wannan annoba.

‘Dan siyasar ya nuna akwai Malaman da ba su yarda da wannan cuta ba, har kuma ya yi kira ga Sheikh Sani Jingir ya dakatar da wa’azin da ya ke yi, inda ya ke karyata cutar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel