Gwamnoni 5 da suka killace Kansu bayan mu'amala da masu coronavirus

Gwamnoni 5 da suka killace Kansu bayan mu'amala da masu coronavirus

Tun farkon samun bullar kwayar cutar coronavirus a Najeriya ta hannun wani dan kasar Italiya, an tabbatar da samun kwayar cutar a jihohin Najeriya 7.

Ya zuwa yanzu kwayar cutar coronavirus ta hallaka mutane 15,000 a fadin duniya, sannan kuma tana cigaba da mamaya a sassan duniya.

Mutum daya ne ya mutu a Najeriya bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus, amma adadin masu dauke da cutar ya kai mutum 46 kuma zai iya karuwa, kamar yadda kididdigar da aka yi da safiyar ranar Laraba, 25 ga watan Maris, ta nuna.

Yawacin mutanen da aka samu suna dauke da kwayar cutar corona a Najeriya, 'yan kasa ne da suka dawo daga kasashen ketare, musamman turai.

A tsakanin manyan jami'an gwamnatin Najeriya, Shugaban ma'aikatan farar shugaban kasa; Abba Kyari, shine na farko da aka fara tabbatarwa yana dauke da kwayar cutar. Na biyu shine gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, sai kuma kakakin majalisar jihar Edo.

1. Bala Mohammed: Duk da an tabbatar da cewa yana dauke da kwayar cutar coronavirus, amma tun kafin a sanar da sakamakon gwajinsa ya killace kansa.

Gwamnoni 5 da suka killace Kansu bayan mu'amala da masu coronavirus
Gwamnoni 5 da suka killace Kansu bayan mu'amala da masu coronavirus
Source: UGC

2. Gwamnan jihar Nasawara, Abdullahi Sule: Abdullahi Sule ya dauki matain killace kansa tare da cigaba da gudanar da aiki daga gida domin ya rage cudanya da jama’a, don gudun kada kuma ya kamu, kamar yadda wata sanarwa daga gwamnatin jihar ta bayyan.

Sanarwar ta kara da cewa: “Idan za’a tuna, Gwamna Sule da kansa ya gayyaci jami’an NCDC zuwa fadar gwamnatin jahar domin su gudanar da gwajin cutar a kansa, amma dukkanin gwaje gwajen da aka gudanar sun nuna baya dauke da ita.

“Za’a cigaba da sanar da jama’a duk wani cigaba da aka samu game da matsayin lafiyar mai girma Gwamna Abdullahi Sule.”

DUBA WANNAN: Jerin jihohin Najeriya 7 da aka tabbatar da bullar kwayar cutar coronavirus

3. Gwamna jihar Neja, Abubakar Sani Bello: Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya killace kansa sakamakon halartan taron kungiyar gwamnonin Najeriya da aka gudanar ranar 18 ga Maris 2020.

Gwamnan ya bukaci killace kansa ne bayan daya daga cikin wadanda suka halarci taron da shi, wato gwamnan jihar Bauchi, Balam Mohammed, an tabbatar da cewa ya kamu da kwayar cutar coronavirus.

Sakataren yada labaran gwamnan, Mary Noel Berje, ta bayyana hakan a jawabin da ta saki ranar Laraba.

4. Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi: Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana cewa ya killace kansa na tsawon makonni biyu bayan haduwa da mutane biyu da aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar Coronavirus.

Gwamnan ya bayyana hakan ne shafinsa na Tuwita a ranar Laraba, 25 ga watan Maris, 2020.

5. Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu: Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya shiga halwa inda ya kebance kansa domin kauce ma yada cutar Coronavirus wanda ake tunanin zai iya kamuwa da ita sakamakon mu’amalar da ya yi da gwamnan jahar Bauchi, Bala Muhammad.

Sahara Reporters ta ruwaito baya ga shiga halwa, gwamnan ya soke dukkanin sha’ani da suka shafe shin a tsawon kwanaki 14, wannan ya biyo bayan gwajin da aka yi ma Bala Muhammad, wanda sakamakon ya nuna Bala ya kamu da cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel