An yi wata ganawa tsakanin Ganduje, Tinubu, Ajimobi da Sanwo-Olu a Legas

An yi wata ganawa tsakanin Ganduje, Tinubu, Ajimobi da Sanwo-Olu a Legas

Mun samu labari cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sake haduwa da Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Legas.

Kamar yadda mu ka samu labari, gwamnan na Kano ya kai wa Asiwaju Bola Tinubu ziyara ne har gidansa, inda ya kuma samu damar ganawa da wasu manyan APC.

Darekta Janar na yada labarai a gidan gwamnatin jihar Kano, Malam Salihu Tanko Yakassai ne ya bayyana wannan ta dandalin shafinsa na Tuwita a Ranar Lahadi.

Hotunan da Salihu Tanko Yakassai ya fitar sun nuna cewa an yi wannan ganawa ne tsakanin Mai gidansa da sauran kusoshin na APC a karshen makon da ya gabata.

Mai girma Abdullahi Ganduje ya kuma samu ganawa da Takwaransa Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, wanda shi ma ya na gidan jagoran APC a lokacin.

KU KARANTA: Shugaban APC Oshiomhole ya bukaci a rufe Sakatariyar Jam'iyya

An yi wata ganawa tsakanin Ganduje, Tinubu, Ajimobi da Sanwo-Olu a Legas

Ganduje tare da Tinubu, Ajimobi da Sanwo-Olu da Obasa
Source: Instagram

Haka zalika Dr. Abdullahi Ganduje ya hadu da tsohon gwamnan jihar Oyo watau Sanata Abiola Ajimobi. Tsohon gwamnan dai Suruki ne wajen Abdullahi Ganduje.

Fatima Abdullahi Ganduje ta na auren Abolaji Abiola Ajimobi. Yanzu haka Abiola Ajimobi ake sa ran zai zama mataimakin shugaban APC na reshen Kudancin Najeriya.

A wannan ganawa ta musamman gwamnan ya samu damar haduwa da Mudathir Obasa, wanda shi ne shugaban majalisar dokokin jihar Legas, kuma na-kusa da Tinubu.

Wata guda kenan yanzu da Abdullahi Ganduje ya yi irin wannan ganawa da Bola Tinubu a gidansa. A duk zaman, ba a san dai abin da ‘Yan siyasar su ka tattauna ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel