Atiku ba za su iya tsayawa zabe idan aka yi wa dokokin takara garambawul ba

Atiku ba za su iya tsayawa zabe idan aka yi wa dokokin takara garambawul ba

Bisa dukkan alamu, kudirin da ke gaban Majalisar Dattawa a yanzu, zai iya kawowa manyan ‘Yan siyasa irinsu Alhaji Atiku Abubakar matsala a zabukan da za a yi nan gaba.

Majalisar Dattawan Najeriya ta na so ayi wa dokokin kasar nan garambawul ta yadda zai zama sai mutum ya mallaki akalla babbar Difloma kafin ya nemi kujerar shugaban kasa.

Wannan kudiri na Sanatan jam’iyyar PDP watau Istifanus Gyang zai yi aiki a kan masu neman takarar gwamnonin jihohi idan majalisa ta amince da shi, har ya zama dokar kasa.

Tuni dai wannan kudiri na Gyang mai wakiltar Kudancin jihar Filato ya tsallake matakin farko a majalisar dattawan. Ana sa rai nan gaba kadan za a sake tattaunawa a kan sa.

A halin yanzu sashe na 131 na kundin tsarin mulki ya bada dama ga duk wanda ya yi karatun sakandare, ya fito takarar shugaban kasa, abin da ake shirin yi wa garambawul.

KU KARANTA: Aisha Buhari ta yi magana bayan Atiku ya kamu da Coronavirus

Atiku ba za su iya tsayawa zabe idan aka yi wa dokokin takara garambawul ba
Majalisar Dattawa ta na so 'Dan takarar Shugaban kasa ya mallaki akalla HND
Asali: UGC

Sanatan ya na ganin cewa akwai bukatar ayi wa wannan sashe na dokar kasar kwaskwarima ta yadda za a ce duk wanda zai rike mulkin Najeriya ya kasance ya na da ko da HND.

Jaridar Vanguard ta ce idan har aka amince da wannan kwaskwarima a kundin tsarin mulki, Atiku Abubakar ya na cikin wadanda wannan aiki zai yi wa tasiri a siyasar kasar.

Ko da Atiku Abubakar bai nuna cewa zai yi takara a 2023, akwai masu ganin har yanzu bai fitar da rai ba. Rahoton ya nuna cewa Atiku bai yi karatu zuwa matakin babban Difloma ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma ‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2019, Atiku Abubakar, ya na da shaidar karamar Difloma ne daga Jami’ar ABU Zariya.

Akwai manyan ‘yan siyasan da ake ji da su a Najeriya da ba su da shaidar HND. Wannan kudiri zai iya hana su takara a 2023. Sai dai wasu sun fara maraba da wannan shiri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel