Hanyar da aka bi aka dinke barakar da ta barkowa Oshiomhole a Jam’iyyar APC

Hanyar da aka bi aka dinke barakar da ta barkowa Oshiomhole a Jam’iyyar APC

Jaridar This Day ta fitar da wani dogon rahoto game da yadda aka kawo karshen rikicin cikin gidan jam’iyyar APC da ya nemi ya ci shugaban jam’iyya na kasa, Adams Oshomhole.

Yayin da ake shirin yin taron majalisar NEC na APC ne sai kwatsam aka ji daga bakin Sakataren rikon kwarya, Cif Victor Giadom, cewa an dakatar da wannan taro sai wani lokaci.

Victor Giadom ya bada wannan sanarwa ne a daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin jihohin APC wadanda su ka bada wannan shawara.

Bayan nan ne kotun daukaka kara ta yanke hukuncin cewa Adams Oshiomhole ya koma kan kujerarsa. A sakamakon haka ne majalisar NWC a karkashin Oshiomhole washegari.

Bayan Adams Oshiomhole ya koma kan kujerarsa, ya nuna cewa shugabannin jam’iyyar su manta da abin da ya faru a baya, su tunkari gaba domin ganin cigaban jam’iyyar mai mulki.

KU KARANTA: Tarihin silar rigimar cikin gidan APC a Jihar Zamfara a zaben 2019

Hanyar da aka bi aka dinke barakar da ta barkowa Oshiomhole a Jam’iyyar APC

Oshiomhole ya nemi ya rasa kujerarsa a rigimar Jam’iyyar APC
Source: UGC

Bayan taron na NWC, Oshiomhole ya bayyana cewa ‘Ya ‘yan APC za su janye duk wasu kara da su ka kai shugabannin jam’iyya a kotu, a haka ne za ayi sulhu cikin gida salin-alin.

An shawo kan sabanin da ya shiga jam’iyyar ne bayan da aka bankara Oshiomhole ya hakura da nada Arch. Waziri Bulama a matsayin sabon Sakataren jam’iyyar APC na kasa.

Shugaban APC na Arewa maso Gabas, Salihu Mustapha wanda ya nuna cewa ba su tare da Waziri Bulama, ya yi nasara, kuma an ba shi damar kawo wanda zai zama Sakataren.

Haka zalika a Kudancin Najeriya, gwamna Kayode Fayemi na Ekiti ya amince da zaben Abiola Ajimobi da ake kokarin yi a matsayin wanda zai maye gurbin Cif Niyi Adebayo.

Rahoton ya bayyana cewa akwai wasu sharudan na dabam da aka gindaya shugabannin APC kafin a cin ma matsaya. Bisi Akande ya na cikin wadanda su ka taka rawar gani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel