Legas ta sha gaban Jihohin Najeriya a barnar annobar Coronovirus

Legas ta sha gaban Jihohin Najeriya a barnar annobar Coronovirus

A halin yanzu cutar nan ta Coronavirus ta shigo har Najeriya inda aka samu tsirarrun mutane da su ka kamu. Mun kawo jerin Jihohin da ake zargin wannan cuta da shiga.

1. Ekiti: A jihar Ekiti an samu labarin bullar cutar daga wani Direba da ya tuka wani Ba-Amurke daga Makwabta Ibadan a jihar Oyo.

2. Edo: A Edo an samu wani Mutumi da ake tunanin ya kamu da cutar, yanzu haka ana kokarin tabbatar da halin da ya ke ciki.

3. Enugu: Gwajin da aka yi ya nuna cewa babu wanda ya kamu da cutar a Enugu. Da farko an yi tunanin COVID-19 ta kama wani.

4. Filato: Jama’a sun shiga halin dar-dar a Filato bayan zargin mutane 43 da kamuwa da cutar. Gwaji ya nuna cutar ba ta kai can ba.

5. Katsina: A jihar Katsina, an tabbatar da cewa babu wanda ya kamu da cutar bayan an yi gwaji a kan wanda aka yi tunanin ya kamu.

6. Kano: Haka zalika a Kano, babu mai dauke da cutar COVID-19. Koda yake ana yada labaran bogi na cewa cutar ta shiga jihar.

KU KARANTA: Coronavirus ta shiga Jihohi 5 a Najeriya amma Shugaba Buhari bai ce uffan ba

7. Legas: Rahotanni sun nuna cewa a Legas ne cutar ta fi samun wuri. Akalla mutane takwas ake zargin sun kamu da wannan cutar.

8. Ogun: A jihar Ogun, bai wuce mutum biyu kawai ke dauke da cutar a yanzu ba. Amma tuni aka tsaurara matakai na hana yaduwarta.

9. Yobe: Babu wani takamaimen wanda aka samu dauke da cutar COVID-19. Har yanzu dai kila-wa-kala ake yi a jihar ta Arewa maso gabas.

10. Ondo: Akwai wanda ake zargin ya na dauke da cutar a Akure. Amma ba a kammala gwaji domin tabbatar da halin da ake ciki ba tukuna.

11. Oyo: Gwajin da aka yi ya tabbatar da cewa cutar COVID-19 ta shiga jihar Oyo. Akwai mutum daya da yanzu ya kamu da wannan cuta.

Bayan wadannan jihohi kuma akwai babban birnin tarayya Abuja, inda kawo yanzu aka samu mutane uku dauke da cutar. A dalilin haka aka rufe makarantun Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng