Bagudu, Ekweremadu, Etete, da mutane 334 su na da kadarorin N152b a Dubai

Bagudu, Ekweremadu, Etete, da mutane 334 su na da kadarorin N152b a Dubai

Gwamna Atiku Bagudu da Sanata Ike Ekweremadu su na cikin wadanda aka ambaci sunayensu a jerin ‘Yan siyasar Najeriyar da su ke dankare da gidaje da kadarori a boye a kasar UAE.

A wani bincike da wani Mutumin kasar waje mai suna Mathew Page, ya yi a kan shugabannin Najeriya, ya gano cewa akalla ‘Yan kasar 331 da su ka tara dukiya a kasar Larabawan.

Mista Mathew Page ya bayyana cewa wadannan Bayin Allah sun mallaki dukiyar Dala miliyan 400 watau N152b a UAE. Daga cikin wadanda aka ambata akwai Jiga-jigan PDP da APC.

Wata Jarida ta bayyana cewa daga cikin wadanda lambarsu ta fito akwai Sanata Atiku Abubakar Bagudu wanda yanzu haka shi ne gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban gwamnonin APC.

Atiku Bagudu ya na da gidaje akalla takwas a Dubai wanda kudinsu ya kai Dala miliyan 4.8. Haka shi ma tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, ba a bar shi a ba yaba.

Ike Ekweremadu ya na da gidaje da aka yi lissafin kudinsu a Dala miliyan 7, Sanatan ya mallaki gidajen ne a wani wurin shakatawa da kuma Burj Dubai. Bayan haka ya na da gidaje a Ingila.

KU KARANTA: Jerin Kasashen da su ka fi dadin rayuwa a Duniya

Bagudu, Ekweremadu, Etete, da mutane 334 su na da kadarorin N152 a Dubai
Ana zargin cewa Sanata Ike Ekweremadu ya na da gidaje a Birtaniya da UAE
Asali: UGC

Binciken ya nuna cewa akwai tsofaffin Gwamnoni da Sanatoci, da kuma Kwamishinoni, da shugabannin hukumomin gwamnati da ‘yan canji da su ka mallaki kadarori a kasar ta UAE.

Sauran manyan Najeriya da ake zarginsu da dukiyoyi a Dubai sun hada da tsohon shugaban PDP, Ahmadu Ali, tsohon gwamnan Kwara, Mohammed Lawal da tsohon Minista Dan Etete.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ibrahim Mantu ya na cikin wadanda aka ambaci sunansu. Haka zalika tsoshuwar shugabar bankin nan na Oceanic, Cecilia Ibru.

Har ila yau a wannan jeri akwai Tafa Balogun wanda ya rike IGP a Najeriya, da kuma Bala Mshelia, da tsohon shugaban NNPC Ladan Shehu da Takwaransa na PPMC, Samuel Okeke.

Rahoton binciken ya ambaci tsohon gwamnan Delta, James Ibori wanda aka taba daurewa a kurkuku. A takaice dai mutane 156 sun mallaki gidaje da kadarori 226 a Garin na Dubai.

Wannan rahoto ya ambaci gwamnoni 35, ‘Yan majalisa 45 da shugabannin ma’aikatu 14. Akwai kuma sunayen tsofaffin Ministoci 15 da Ma’aikatan NNPC da fadar shugaban kasa da Alkalai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng