Hanin da aka yi wa tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II baiwa ne – inji Umar Ardo

Hanin da aka yi wa tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II baiwa ne – inji Umar Ardo

Dr. Umar Ardo wanda fitaccen ‘Dan siyasa ne kuma Masani a Arewacin Najeriya, ya yi hira da Jaridar Daily Trust inda ya tabo batun 2023 da kuma tsige Sarkin Kano da aka yi.

A na sa ra’ayin Umar Ardo ya na ganin cewa gwamnatin APC ta buga katabora wajen tsige Muhammadu Sanusi II da kuma barka masarauta da Gwamnatin Kano ta yi a 2019.

A siyasarsu ta PDP kuwa, Jagoran jam’iyyar ya na ganin cewa Muhammadu Sanusi II zai iya zama kadara ga jam’iyyar PDP, wanda ya ce tunbukesa da aka yi zai iya zama masa alheri.

Dr. Ardo ya bayyana cewa ya na da ra’ayin bai kamata a fara maganar takarar Muhammadu Sanusi II a yanzu ba, ya ce ya kamata ne a wannan lokaci tsohon Sarkin ya wartsake tukuna.

“Ina son shi, kuma ina ganin cewa za ayi dacen shugaban kasa idan ya samu mulki. Idan har ya ji maganar mutane ya tsaya takara, zai ci zabe. Ina maso kallon cewa zai kai labari.” Inji sa.

KU KARANTA: Sanusi II ba zai bukaci kotu ta maida shi kan gadons sarauta ba

Hanin da aka yi wa tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II baiwa ne – inji Umar Ardo
Umar Ardo ya ganin Muhammadu Sanusi II zai yi kyau da shugaban kasa
Asali: Depositphotos

Sai dai idan har tsohon gwamnan babban bankin zai shiga siyasa, Ardo ya na ganin jam’iyyar PDP mai adawa ce ta fi dacewa da shi ba jam’iyyar APC ta Abokinsa Gwamna Nasir El-Rufai ba.

“A wani bangaren, cire masa rawani ya na iya zama mafitar matsalolin shugabancin Arewa. Duk mun san cewa Arewa ta dade ta na neman shugaba, eh mun san ‘Dan Arewa ya ke mulki.”

‘Dan siyasar ya kara da cewa: “Amma gazawarsa na kawo karshen matsalolin kasar musamman na Yankin Arewa, game da tsarin shugabancinsa (Buhari) ya sa ‘Yan Arewa sun ji kunya”

Ya ce: “Duk inda Sanusi II ya je, magana daya ce, ana sukar aikin gwamnatin APC. Jama’a sun buge da neman Jagora, kuma kamar tunbuke Sanusi II ya sa an fara yi masa wannan kallo”

Jigon adawar ya ce Sanusi II zai samu karbuwa a Arewa da Kudancin Najeriya, haka wajen ‘Yan zamani da kuma gidajen sarauta da Talakawa, da kuma goyon baya daga manyan Duniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel