Jigon APC a Kaduna ya maidawa Kano martani a kan batun Sanusi II

Jigon APC a Kaduna ya maidawa Kano martani a kan batun Sanusi II

Wani daga cikin manyan Jagororin jam’iyyar APC a Kaduna, Yusuf Ali, ya maidawa reshen jam’iyyar na jihar Kano martani game da wasu maganganu da su ka yi.

A farkon makon nan ne jam’iyyar APC ta jihar Kano ta fito ta na sukar yadda gwamnan jihar Kaduna ya yi wa Muhammadu Sanusi II kara bayan an tube masa rawani.

Idan ba ku manta ba, a Ranar 9 ga Watan Maris, gwamnatin Kano ta tunbuke Muhammadu Sanusi II daga kujerar Sarki. Nasir El-Rufai ya nunawa tsohon Sarkin hallaci.

Alhaji Yusuf Ali wanda aka fi sani da Rabagardama ya bayyana jam’iyyar ta APC ta reshen Kano a matsayin tarin mutane marasa godiya na kokarin takalar Nasir El-Rufai.

Yusuf Ali ya ke cewa jam’iyyar APC ta Kano ta yi saurin mantawa da irin yadda gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya bada gudumuwa wajen cigaban jihar ta Kano.

KU KARANTA: El-Rufai ya yi magana game da mukaman da ya ba Sanusi II

Jigon APC a Kaduna ya maidawa Kano martani a kan batun Sanusi II

Jagoran APC ya yi wa Gwamnatin Ganduje gorin abin ya El-Rufai ya yi masu
Source: UGC

“Mun karanta bayanin takaicin da wani Shehu Maigari daga ofishin jam’iyyar APC a jihar Kano ya yi kokarin yi a wasu shafukan jaridu, ya na sukar goyon baya da kaunar da gwamna El-Rufai ya nunawa Abokinsa, tsohon Sarkin Kano, Mai martaba Muhammadu Sanusi II.”

“Wannan ya nuna cewa taimakawa APC ta Kano tamkar ba kaza abinci ne sannan ta goge baki, domin ba za su gode ko su yabawa rawar da El-Rufai ya taka a Kano a 2019 ba.”

A cewarsa, El-Rufai ya ba jam’iyyar APC gudumuwa a lokacin da ta shiga mafi kalubalen lokaci a zaben Kano a 2019. Wannan ya gaskata rade-radin tsoma bakin a zaben Kano.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel