Dalilin da ya sa na ajiye sarautar da Sanusi II ya bani – Naziru sarkin waka

Dalilin da ya sa na ajiye sarautar da Sanusi II ya bani – Naziru sarkin waka

Fitaccen mawakin nan na Kannywood Naziru M. Ahmad wanda aka fi sani da sarkin wakar sarkin Kano, ya bayyana gaskiyar dalilin da ya sa ya ajiye mukamin da tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bashi bayan dakatar dashi.

A wata hira da ya yi da shafin BBC Hausa, Mawakin ya bayyana cewa ya yi murabus ne saboda sarautar tasa na da alaka da wanda ya nada shi, wato Sanusi na II.

Ya kuma jadadda cewa wannan mataki nasa ba yana nufin cewa yana adawa da sabon sarkin Kanon bane.

Dalilin da ya sa na ajiye sarautar da Sanusi II ya bani – Naziru sarkin waka
Dalilin da ya sa na ajiye sarautar da Sanusi II ya bani – Naziru sarkin waka
Asali: Twitter

A makon jiya ne gwamnatin jahar Kano karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ta sauke Muhammadu Sanusi na II daga kan mulki bayan ta zarge shi da rashin biyayya.

Daga nan ne aka kai tsohon sarkin jihar Nasarawa amma daga bisani kotu ta umarci a sake shi inda ya tafi jahar Lagos.

Naziru M. Ahmad dai shi ne ya wake tsohon sarkin Kano Sanusi na II a cikin fitacciyar wakarsa ta 'Mata ku dau turame'.

Idan za ku tuna a baya mun kaw maku labarin yadda Nazir Ahmad Sarkin Wakar San Kano ya ajiye mukaminsa da tsohon Sarki Sanusi ya bashi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takarda da ke ta faman karakaina a shafukan sadarwa na zamani.

Takardar wacce aka rubuta ta a ranar 13 ga watan Maris dinnan tayi bayani kamar haka:

"Bismillahir Rahamanir Rahim! "

Na rubuta wannan takarda domin na sanar da hukuncin dana yanke na yin murabus daga mukamina na 'Sarkin Wakar San Kano', wanda zai fara daga yau 13 ga watan Maris na shekarar 2020. Ina godiya matuka akan wannan mukami da aka bani ba wai iya ga masarautar Kano ba, ina godiya ga jihar baki daya.

"Haka kuma, ina godiya ga masarautar da irin damar da ta bani na yin aiki da ita tsawon shekara daya da wani abu, wannan wata dama ce dana samu da kuma zan cigaba da cin ribarta har karshen rayuwata.

"Ina fatan zaku yi na'am da wannan hukunci da godiya tawa.

"Na ku a koda yaushe,

"Alhaji Nazir Muhammad Ahmad."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng