Yanzu Yanzu: Majalisa ta bukaci Buhari ya yi jawabi ga al’umman Najeriya kan coronavirus

Yanzu Yanzu: Majalisa ta bukaci Buhari ya yi jawabi ga al’umman Najeriya kan coronavirus

- Majalisar dattawa ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi jawabi ga yan Najeriya kan annobar coronavirus

- Shugaba Buhari dai bai ce wa al'umman kasar komai ba tun bayan barkewar annobar makonni uku da suka gabata

- A yanzu an tabbatar da samun mutane akwas da ke dauke da cutar a Najeriya

- Majalisar ta kuma bukaci samar da cibiyoyin gwaji a dukkanin jihohi 36 da babbar birnin tarayya

Majalisar dattawa ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi jawabi ga yan Najeriya kan annobar coronavirus.

Majalisar ta gabatar da wannan bukata ne bayan tafka muhawara kan muhimmancin hakan ga al’umma a ranar Laraba, 18 ga watan Maris a zauren majalisa.

A yanzu haka Najeriya ta tabbatar da lamarin cutar a jikin mutane takwas a kasar.

Har yanzu Shugaban kasar bai yi jawabi ga al’umman kasar ba tun bayan barkewar annobar, koda dai an samu lamarin na farko a kasar tun makonni uku da suka gabata.

Yanzu Yanzu: Majalisa ta bukaci Buhari ya yi jawabi ga al’umman Najeriya kan coronavirus

Yanzu Yanzu: Majalisa ta bukaci Buhari ya yi jawabi ga al’umman Najeriya kan coronavirus
Source: UGC

Majalisar ta kuma bukaci samar da cibiyoyin gwaji a dukkanin jihohi 36 da babbar birnin tarayya.

Ta kuma nemi wajabta kebe kai ga matafiya daga kasashen da ke da yawan wadanda suka kamu.

KU KARANTA KUMA: Yajin aiki: Mun cimma yarjejeniya kwakkwara da gwamnatin Najeriya - ASUU

A baya mun ji cewa gwamnatin tarayya ta haramtawa matafiya daga kasashe 13 shigowa Najeriya daga yau saboda annobar cutar Coronavirus. Gwamnatin ta yanke wannan shawara ne domin takaita yaduwar cutar a Najeriya. Kawo yanzu, mutane uku kacal aka tabbatar da sun kamu da cutar a Najeriya.

Kasashen da aka haramtawa shiga Najerya sune Sin, Italiya, Iran, Koriya ta kudu, Andalus (Spain), Japan, Faransa, Jamu, Amurka, Norway, Ingila, Holand, da Swizalan.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta bayyana hakan ne da safiyar Laraba, 18 ga Maris, 2020.

Jawabin yace “Gwamnatin tarayya ta hana shigowa kasar ga matafiya daga kasashen Sin, taliya, Iran, Koriya ta kudu, Andalus (Spain), Japan, Faransa, Jamu, Amurka, Norway, Ingila, Holand, da Swizalan.“

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel