Okechukwu ya yi wa Tinubu raddi, ya ce Oshiomhole ne matsalar Jam’iyyar APC
Darekta Janar na hukumar gidan rediyon kasa na VON, Osita Okechukwu, ya maidawa Jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu martani game da kalaman da ya yi a karshen makon jiya.
Jaridar Daily Trust ta rahoto Osita Okechukwu ya na fadawa Duniya cewa Adams Oshiomhole ne babbar matsalar da ke cikin tafiyar APC, akasin abin da Bola Ahmed Tinubu ya bayyana.
Bola Ahmed Tinubu ya yi magana ya na cewa wadanda ke ta kokarin sauke Adams Oshiomhole daga kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa, sun kamu ne da kwayar cutar zaben 2023.
Da ya ke maida martani a babban birnin tarayya Abuja a Ranar Litinin, 16 ga Watan Maris, 2020, Okechukwu ya ce Kmwared Adams Oshiomhole ne kwayar cutar da ta kama jam’iyyar.
“Tare da ganin girmar Jagoranmu na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mu ‘yan kishin jam’iyyar APC ne masu Magoya baya a kasa. A ba mu dama mu fito baro-baro mu bayyana cewa mun dauki Adams Oshiomhole a matsayin mutum mai daraja, kuma mun ci burin cewa zai yi aiki nagari a shugabancin da ya ke yi. Wannan ya sa ‘Ya ‘yan APC a fadin kasa su ka fito su ka mara masa baya ya zama shugaban jam’iyya shekaru biyu da su ka wuce ba tare da hamayya ba.”
KU KATANTA: Yunkurin tunbuke Oshiomhole ya faskara bayan an kira taron NWC
“Don haka bayan shekaru biyu a bakin aiki, cikin takaici mu ke cewa Adams Oshiomhole ya rusa duk burin da mu ka yi a kansa, ya yi watsi da kundin tsarin mulkin APC da nauyin da aka damka masa, ya aikata wasu manyan laifuffuka goma da su ka sabawa jam’iyyarmu ta APC.”
Okechukwu ya kara da cewa: “Idan har akwai wata kwayar cuta kamar yadda Mai daraja Bola Tinubu ya ke ikirari, to za ta zama kwayar cutar Oshiomhole ce, ba wai cutar 2023 ba.”
Daga cikin laifuffukan da Okechukwu ya ke zargin Oshiomhole da su akwai sabawa dokar jam’iyya, babbako da PDP, da kuma kawo matsala a zabukan tsaida ‘Dan takara.
Haka zalika Okechukwu ya zargi munafuntar shugaba Buhari da nakasa kuri’unsa a zaben 2019. A cikin ‘yan kwanakin nan ne ya zargi shugaban jam’iyyar da yaudar Bola Tinubu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng