Ganduje da Fayemi: Sarakunan Ibadan za su gana da Muhammadu Sanusi II a Legas

Ganduje da Fayemi: Sarakunan Ibadan za su gana da Muhammadu Sanusi II a Legas

A Ranar Litinin ne Gungun Sarakunan kasar Ibadan wanda da ake kira Mogajis su ka gargadi Mai girma gwamnan Ekiti game da shirin da ya ke yi na tsige Sarakunan jiharsa.

Sarakunan gargajiyar sun ja kunnen gwamna Kayode Fayemi da cewa ka da ya sake ya kawo masu bakuwar dabi’a a wannan zamani na tunbuke masu mulki a kasar Yarbawa.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust, wadannan masu iko sun bayyanawa gwamnan na APC cewa tsige Sarakunansa 11 ya na da hadari a kasar ta Yamma.

Manyan Sarakan sun yi magana ne ta bakin Mai magana da yawunsu watau Cif Wale Oledoja wanda ya tunawa gwamnonin Ekiti da Kano cewa wa’adinsu fa kayyadadde ne.

Wale Oledoja ya ce yayin da gwamnoni irin Kayode Fayemi da Abdullahi Ganduje ba su iya zarce shekaru takwas a kan mulki, Sarakuna kuwa su na iko ne har sai sun bar Duniya.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ba ta ji dadin yadda El-Rufai ya marawa Sanusi II baya ba

Ganduje da Fayemi: Sarakunan Ibadan za su gana da Muhammadu Sanusi II a Legas

Ana rade-radin Gwamna Fayemi ya na shirin tsige wasu Sarakunan Ekiti
Source: Twitter

Wadannan Sarakai da ake ji da su a kasar sun kuma nuna cewa sun shirya kai wa tsohon Sarkin Birnin Kano da aka tunbuke, Muhammadu Sanusi II, ziyara a halin yanzu.

“Mafi yawan Sarakunan nan sadaukar da rayuwarsu ne don haka su ke bukatar a ba su girma, Ka da Fayemi ya dauko mana bakuwar siyarsar gaba daga wasu Kabilu.”

“Mu na ganin girman Sarakunan mu a kasar Yarbawa, kuma ba za mu yi wani abu da zai cuta masu ba.” Oladoja ya kuma yi magana game da Gwamnan jihar Kano.

“Ganduje shi ne gwamna yau, watakila ba shi ba ne a kujerar gobe. Ka da ya ruguza gidan sarautar Kano kafin ya bar ofis. Yaushe zama laifi ga Sarakuna su fadi gaskiya?”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel