Shugaban APC Oshiomhole ya zauna da Kyari ana tsakar rigimar cikin-gida

Shugaban APC Oshiomhole ya zauna da Kyari ana tsakar rigimar cikin-gida

Labari ya zo mana daga gidajen Jaridu da-dama cewa shugaban jam’iyyar APC mai mulki, Adams Oshiomhole, ya kai ziyara zuwa fadar shugaban kasa a Ranar Litinin.

Kamar yadda mu ka samu labari, Kwamred Adams Oshiomhole ya samu ganawa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa watau Alhaji Abba Kyari a ziyarar da ya kai.

Sai dai Oshiomhole bai iya haduwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, wanda a lokacin ana tunanin ya na tare da shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamilla.

Bayan ya gana da Rt. Hon. Femi Gbajabiamilla, shugaban kasar ya halarci bikin Expo 2020 wanda ma’aikatar kimiyya da fasaha ta shirya a filin Eagles Square da ke Garin Abuja.

KU KARANTA: An dakatar da zaman NEC bayan Oshiomhole ya yi nasara a kotu

Shugaban APC Oshiomhole ya zauna da Kyari ana tsakar rigimar cikin-gida

Oshiomhole ya gana da Abba Kyari a fadar Aso Villa
Source: Depositphotos

Wata majiya daga cikin fadar shugaban kasar ta ce Adams Oshiomhole ya shiga ofishin Abba Kyari ne da rana. ‘Yan jarida ba su iya samun labarin wannan tattaunawa ba.

Ko da shugaban na APC na kasa bai yi wa Manema labarai magana game da wannan zama ba, Legit.ng Hausa ta fahimci cewa zaman bai rasa nasaba da rikicin cikin gida.

Oshiomhole ya ziyarci fadar shugaban kasar ne jim kadan bayan kotun daukaka kara ta yanke hukunci, ta ba shi nasara bayan an dakatar da shi daga kujerarsa a makon jiya.

Bayan Alkali ya dakatar da Oshiomhole kwanaki, shugaban jam’iyyar ta APC na kasa ya nuna cewa wani Ministan Buhari ne da gwamnonin APC su ka yi masa wannan aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel