El-Rufai: Ka kirkirowa Muhammadu Sanusi II wata Masarauta a Kaduna – Kano APC

El-Rufai: Ka kirkirowa Muhammadu Sanusi II wata Masarauta a Kaduna – Kano APC

Jam’iyyar APC ta reshen jihar Kano ta fito ta yi magana game da huldar da ke tsakanin gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da kuma Malam Muhammadu Sanusi II.

APC ta jihar Kano ta yi kira ga Mai girma gwamnan Kaduna watau Nasir El-Rufai ya kafa wata sabuwar masarauta ya kuma ba tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II rikonta.

Jam’iyyar mai mulki ta yi wannan maganar ne bayan ganin yadda Gwamnan na Kaduna ya rika nuna goyon bayansa ga tsohon Sarkin na Birnin Kano Muhammadu Sanusi II.

A makon da ya gabata Gwamna El-Rufai ya nada tsohon Sarkin a matsayin Shugaban jami’ar KASU, hakan na zuwa ne bayan ya nada shi cikin majalisar hukumar KADIP.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Kano, Alhaji Shehu Maigari, ya na fadawa El-Rufai cewa tsohon Sarkin ya yi wa PDP aiki ne a zaben 2019.

KU KARANTA: El-Rufai ya ba ni labarin Abokantakarsa da Uba na – Yusrah Sanusi

El-Rufai: Ka kirkirowa Muhammadu Sanusi II wata Masarauta a Kaduna – Kano APC

Kano APC ta ce Gwamna El-Rufai ya ba Muhammadu Sanusi II sarauta a JIharsa
Source: Twitter

“Mai girma Gwamna Nasir El-Rufai, wannan mutum ne wanda ya yi aiki domin hana APC, jam’iyyarka samun nasara, ya fito fili ya na sukar gwaninka Shugaban kasa.”

Jawabin ya kara da cewa: “Ba tare da wata hujja ko dalili mai gamsarwa ba. Amma ka zabi ka rika daukarsa wani Gwarzo.” A karshe Jigon na APC ya ba gwamnan shawara.

“Ran ka ya dade, jam’iyyar APC ta na ba ka shawarar ka kirkiri sabuwar masarauta a jihar Kaduna, wanda watakila za ta yi iko daga kasar Rigachikun zuwa Kasuwar Magani.”

“Sai ka nada Gwaninka a kan sarautar, yadda zai yi wa jam’iyyarsa ta PDP da kyau aiki a can, a maimakon ka rika ba shi wasu mukaman je-ka-na-yi-ka.” Inji Alhaji Shehu Maigari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel