Taron NEC: Wasu Gwamnoni su na goyon bayan Shugaban APC Oshiomhole

Taron NEC: Wasu Gwamnoni su na goyon bayan Shugaban APC Oshiomhole

Yayin da ake shiryawa taron majalisar zartarwa ta APC watau NEC, babban jigon jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, ya nuna cewa ya na goyon bayan Adams Oshiomhole.

Bayan dogon lokaci, Bola Tinubu ya fito ya yi magana, ya na mai sukar wadanda su ke yunkurin tunbuke Adams Oshiomhole daga kujerar da ya ke kai na shugaban APC na kasa.

Tsohon gwamna Bola Tinubu ya na cikin wadanda su ka yi ruwa da tsaki wajen ganin an maye John Odigie-Oyegun da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyya a 2018.

A dalilin haka ne ake tunanin cewa Adams Oshiomhole zai goyi bayan takarar Tinubu idan har ya nuna sha’awar neman tikitin shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a 2023.

Wannan dalili ya na cikin abin da ya sa wasu manyan jam’iyyar APC su ke yunkurin ganin sun tsige Oshiomhole, su nada wani sabon shugaba wanda zai yi irin rawar kidansu.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya amince da zaman NEC a Jam'iyyar APC

Taron NEC: Wasu Gwamnoni su na goyon bayan Shugaban APC Oshiomhole
Maganar kujerar Oshiomhole zai cika taron APC NEC
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta yi bincike ta gano matsayar duka gwamnonin jam’iyyar APC a wannan rikici. Irinsu Hope Hope Uzodinma da Godwin Obaseki su ka bayyana matsayarsu.

Daga cikin gwamnonin da ake ganin cewa su na tare da Oshiomhole akwai: Babagana Zulum Abdullahi Umar Ganduje, Aminu Bello Masari, da Yahaya Bello, da Abdullahi Sule.

Sauran gwamnonin da ke tare da Oshiomhole su ne: Abdulrahman Abdulrazak, Babajide Sanwo-Olu, Hope Uzodinma, Dapo Abiodun, Gboyega Oyetola da kuma Alhaji Mai Mala Buni.

Sauran gwamnonin da ake tunanin cewa ba za su marawa Oshiomhole baya idan an zo taron NEC ba sun hada da: Godwin Obaseki, Kayode Fayemi, Badaru Muhammad, da Nasir El-Rufai.

Haka zalika hasashe ya nuna cewa Atiku Bagudu, Abubakar Sani Bello, Rotimi Akeredolu da kuma Simon Lalong ba su cikin tafiyar Oshiomhole da kuma jigon jam’iyya Tinubu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng