Majalisa: ‘Dan takarar APC Fagen-Gawo ya yi nasara a zaben Babura/Garki

Majalisa: ‘Dan takarar APC Fagen-Gawo ya yi nasara a zaben Babura/Garki

‘Dan takarar jam’iyyar APC a zaben kujerar majalisar tarayya na Yankin Babura da Garki a jihar Jigawa ne ya lashe zaben da aka yi a Ranar Asabar dinnan da ta gabata.

Kamar yadda mu ka samu labari daga hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, Muhammad Fagen-Gawo, ya lashe wannan kujera ta tarayya bayan ya samu kuri’u 48, 318.

An gudanar da wannan zabe ne a rumfuna 302 da ke cikin kananan hukumomin Garki da Babura. Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben ofishinta da ke Babura a jiya.

Farfesa Ahmed Kutama wanda ya yi aiki a matsayin Malamin wannan zabe ya sanar da cewa ‘Dan takarar APC Fagen-Gawo shi ne ya yi galaba a kan sauran ‘Yan takarar.

‘Dan takarar jam’iyyar PDP mai adawa, Nasiru Garba Dantiye, shi ne ya zo na biyu da kuri’a 24, 135. Hakan na nufin akwai ratar kuri’u 24, 183 tsakanin 'Dan takarar APC da PDP.

KU KARANTA: Kan jam'iyyar APC ya rabu game da taron NEC a makon nan

Majalisa: ‘Dan takarar APC Fagen-Gawo ya yi nasara a zaben Babura/Garki

Jam'iyyar APC ta yi nasara a zaben 'Dan Majalisar Babura da Garki
Source: Twitter

Wanda ya zo na uku kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta watau INEC ta sanar shi ne Bashir Umar. Umar wanda ya tsaya takara a ADP ya tashi ne da kuri’a 458.

Hukumar INEC ta gabatar da Malam Muhammad Fagen-Gawo a matsayin wanda ya yi nasara a wannan zabe da aka yi domin cike gurbin kujerar majalisar wakilan tarayyar.

Tun a lokacin da ake gudanar da wannan zabe mu ka samu labari cewa jam’iyyar APC ce ta ke kan gaba. Wani Malamin da ya yi aikin zaben ya shaidawa Legit.ng haka.

Idan ba ku manta ba a Disamban 2019 ne ‘Dan majalisar APC Dr. Muhammadu Adamu Fagengawo ya rasu a kan mulki. Yanzu ‘Dansa ne zai maye gurbinsa a majalisar wakilai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng News

Online view pixel