Mu na da hujjar da ke nuna DSS, Sojoji sun hana ayi zabe da kyau – Amurka

Mu na da hujjar da ke nuna DSS, Sojoji sun hana ayi zabe da kyau – Amurka

Gwamnatin kasar Amurka ta ce akwai hujjar da ke nuna cewa jami’an tsaro wanda su ka hada da Sojoji da DSS sun rika tsoratar da masu zabe da ma’aikata a zaben shekarar bara.

Kasar Amurkan ta nuna cewa Sojoji da Jami’an DSS masu fararen kaya sun hana Malaman zabe yin aikinsu da kyau a zaben 2019. Hakan ya nuna alamun Sojoji sun yi wa APC aiki.

Haka zalika kasar ta Amurka ta nuna cewa akwai alamun shugabanni su na bankara Alkalai. Wannan rashin gaskiya ta fuskar shari’a ya hana kotu ta yi aikin da ya dace a Najeriya.

Wadannan bayanai duk su na cikin rahotannin da ma’aikatar cikin gidan Amurka ta fitar a game da abubuwan da su ka faru a lokacin zaben Najeriya kamar yadda mu ka samu labari.

A rahoton da Amurka ta fitar mai shafi 44, ta ce: “Akwai hujjar da ke nuna cewa Sojoji da sauran jami’an tsaro sun rika razana Masu kada zabe, da Malaman zabe da masu aikin sa-ido.”

KU KARANTA: Harin 2023 ta sa wasu ke neman tunbuke Oshiomhole - Tinubu

Mu na da hujjar da ke nuna DSS, Sojoji sun hana ayi zabe da kyau – Amurka
Amurka ta zargi Jami'an tsaro da budawa jama'a ido a zaben Najeriya
Asali: UGC

“Bayan kuma rikicin da aka tada a jihohi da-dama wanda hakan ya jawo karancin masu fita yin zabe. Wannan ya karawa maganar da ake yi na cewa ana amfani da Sojoji a zabe karfi.”

“Misali hatsaniya da shigar Sojoji cikin aikin zabe wanda su ka hada da tattara kuri’u ya kawo cikas a zaben jihar Ribas. Haka zalika Sojoji sun rika budawa manyan Jami’an INEC ido.”

Rahoton ya cigaba da cewa: “Akwai zargin rashin gaskiya wanda su ka hada sayen kuri’u. An yi wannan a zaben gwamnan Osun a 2018 da kuma zaben gwamnan jihar Kano a 2019.”

Rashin biyan Ma’aikatan shari’a kudi mai tsoka ya sa su ka rika juya gaskiya inji rahoton kasar wajen. “Akwai zargin da ke yawo sosai cewa an biya Alkalai kudi domin sayen shari’a.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel