Junaid Mohammed: Tsohon Sarki Sanusi II bai san al’adun Arewa ba, tashin Legas ne

Junaid Mohammed: Tsohon Sarki Sanusi II bai san al’adun Arewa ba, tashin Legas ne

Tsohon ‘Dan siyasar Arewa, Dr. Junaid Muhammad II, ya yi wata doguwar hira da Jaridar Vanguard, inda ya tofa albarkacin bakinsa game da tunbuke Sarkin Kano da aka yi.

Junaid Muhammad II ya bayyana cewa Sanusi II ba zai iya musanya zargin da ke kan wuyarsa na bata al’adar mutanen Kano ba, domin duk ya aikata wadannan laifuffuka da ake fada.

Mohammed ya ce akwai tafka da warwara a sha’anin Muhammadu Sanusi II ganin yadda ya ke sukar yawan haihuwan yara, alhali shi karon kansa ya na da taron ‘Ya ‘ya 24 a Duniya.

Haka zalika Dr. Mohammed ya zargi Muhammadu Sanusi II da tsilla-tsilla a fuskar akidar addini, inda ya ce yau ba ya tare Mabiya Shi’an Zakzaky, sannan kuma gobe ba ya tare da Izala.

Wannan ne ya ke fadawa mutane ka da su haifi ‘Ya ‘ya da yawa. Mahaifiyarsa kawai ta na da Yara 10. A dalilin haka Mohammed ya ce Sanusi II bai fahimci al’adar Malam Bahaushe ba.

Dattijon ya ce: “Wanda mutum hudu suka nada Sarki ba zai ce shi ne shugaban mutane miliyan 17 ba. Idan bai shirya bin al’adun mutane ba, bai kamata ya zama Sarkin kasar Kano ba.”

KU KARANTA: Allah bai yi zan mutu a kan gadon sarauta ba - Sanusi II

Junaid Mohammed: Tsohon Sarki Sanusi II bai san al’adun Arewa ba, tashin Legas ne
Junaid Mohammed ya ce bai kamata tun farko a nada Sanusi ba
Asali: Facebook

“Shugaban kasa Buhari ya goyi bayan zamansa Sarki, ka je ka ce ni na fada maka wannan. Buhari ya koyi darasi, shiyasa ya janye hannunsa daga siyasar Kano.” Inji Mohammed.

“Idan Magoya bayan Sanusi da ‘Yan jarida sun jahilici lamarin, Buhari ba jahili ba ne. Tsohon Shugaba ne wanda ya san babu yadda za ayi idan har mutanen Kano su ka ce kaza.

Ya na ganin tsohon Sarkin ya cancanci a tsige shi. “Ni a na wa ra’ayin, tsigesa shi ne abin da ya dace. Ya kamata ace an yi wannan tuni. Kai zan ma ce bai kamata ya zama Sarki ba."

“Legas kawai ya sani inda yi rayuwarsa, a wajen gama-garin Bakano, al’adarsa da addini sun fi wani kundin tsarin mulki. An bi tsarin mulki wajen tunbuke shi, kuma ya yarda.”

"Gwamna mai-ci ya rike kujerar mataimakin gwamna, ya yi Kwamishina sau uku. Ya na Digirin PhD a sha’anin mulki, Ko ma menene, mafi yawan jama’a su na tare da shi a nan.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel