Sanusi: Yan sanda sun kama sojan bogi a Awe

Sanusi: Yan sanda sun kama sojan bogi a Awe

Labari da ke zuwa mana ya nuna cewa rundunar yan sandan Najeriya a Awe ta kama wani sojan bogi a safiyar ranar Juma’a, 13 ga watan Maris.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kama shi ne sanye da kaya da takalman sojoji a wani masauki a yankin.

Jami’an yan sanda da ke bakin aiki sun yi masa wasu tambayoyi.

Da aka nemi ya yi bayanin ko shi wanene, sai ya bayyana cewa yana kaan hutu ne kuma cewa ya zo Awe ne domin ganin korarren sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Sanusi: Yan sanda sun kama sojan bogi a Awe

Sanusi: Yan sanda sun kama sojan bogi a Awe
Source: Twitter

Sai jami’an yan sandan suka kira DOP din Awe, Superintendent Augustine wanda ya tafi dashi domin ci gaba da bincike.

Sai dai ba a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jahar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel ba domin bai amsa kiran wayarsa ba.

A halin da ake ciki, mun ji cewa an tsaurara matakan tsaro a garin Awe na jahar Nasarawa, inda aka ajiye korarren sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II tun bayan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano ya tsige shi.

An gano jami’an rundunar sojin Najeriya, jami’an tsaro na yan sandan fari n kaya (DSS), yan sanda da kuma jami’an hukumar Civil Defence zube wadanda ke bayar da kariya ga tsigaggen sarkin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai a wata hira da kwamishinan yan sandan jahar, Bola Longe, ya ce an zuba matakan tsaro ne a karamar hukumar Awe na jahar Nasarawa domin amfanin kowa.

“An zuba Karin jami’an tsaro ne a garin domin su kare mazauna yankin da baki a garin, ba wai don tsorata kowa ba.

KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya kai ma Malam Muhammadu Sunusi II ziyara a Awe

“Ina rokon mutanen Awe masu halin kirki da su bi oda musamman a lokacin sallar Juma’a,” in ji CP Longe a ranar Alhamis.

An tattaro cewa an tsaurara matakan tsaro a garin ne saboda bayyanar da Sanusi zai yi a sallar Juma’a domin jam’i da sauran Musulmai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel