Wasu daga cikin manyan jawaban da Muhammadu Sanusi II ya taba yi a tarihi

Wasu daga cikin manyan jawaban da Muhammadu Sanusi II ya taba yi a tarihi

Bayan gwamnatin jihar Kano ta tunbuke Malam Muhammadu Sanusi II daga kan daga kan gadon sarauta, jama’a sun yi ta fitowa su na tofa albarkacin bakinsu a game da hakan.

Jaridar Daily Trust ta kawo wasu maganganu da tsohon Sarkin ya taba yi wadanda su ka jawo ce-ce-ku-ce a Kano, Arewa da ma kaf Najeriya baki daya. Ga kadan daga cikin jawabansa:

Soyayya da aure

“Mutanenmu su na fuskantar baranza sosai a cikin gida. Mu na yawan samun kukan Mahaifan da ke tursasawa ‘Ya ‘yansu su auri Mazan da ba su so. Mun saba jin wadanda su ka kara aure yayin da ba su iya ciyar ko tufatar ko samawa Matanna su matsuguni.”

Dukan Matan aure

“Na gargadi Hakimaina da Masu Unguwanni da Lawalai har da Limamai game da dukan Matansu. Duk wanda na ji ya bugi matarsa, zai rasa rawaninsa.”

Tallafin man fetur

“Dole a cire tallafin man fetur, a kara fadada samun kudin haraji. Dole a kara harajin VAT. Ba zai yiwu a rika karbar haraji daga kamfanonin mai da na sadarwa ba, amma ace ba a biyan haraji a kashi 60 zuwa 70 na kayan masarufi.”

KU KARANTA: Najeriya Gwamnatin Kano ta yi wa illa ba Sanusi ba - Obi

Wasu daga cikin manyan jawaban da Muhammadu Sanusi II ya taba yi a tarihi

Sanusi II ya yi kaurin suna wajen fadar gaskiya ba tare da tsoro ba
Source: UGC

Shugabanci

“Ba wani sirri ba ne cewa da yawan shugabannin siyasarmu ba su da cikakken ilmi da kuma sanin aiki. ‘Yan Najeriya ba su sa ran ganin wadannan shugabanni sun tubuka wani abin kirki.”

Talauci

“Talauci ya ci kashi 80% na Yankin Arewacin Najeriya; yayin da kashi 20% na ‘Yan Kudu ne kurum su ke cikin talauci. An samu wannan ne saboda yawan auren mata da haihuwar Yaran da a karshe su ke komawa gantali a titi domin neman abinci.”

Gwamnoni

“Mu na da gwamnonin da ke zuwa kasar China, su shafe wata guda su na rangadi, me su ke kawo mana tsaraba? Yarjejeniyar cin bashi. China za ta ba ka aron Dala biliyan 1.8 ka gina dogon jirgin kasa; Jiragen daga China za su zo, Ma’aikatan daga China, ‘Yan kwadagon daga China, Direban jirgin daga China. Me ka tashi da shi?”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel