Messi zai dauki hayar Lauyoyi, ya biyasu Miliyan €4 su fito da Ronaldinho

Messi zai dauki hayar Lauyoyi, ya biyasu Miliyan €4 su fito da Ronaldinho

Rade-radi su na zuwa mana cewa fitaccen ‘Dan wasan Duniya, Lionel Messi ya shirya kashe kudi masu yawo domin a fito da Ronaldinho daga hannun hukuma.

Idan ba ku manta ba, tsohon ‘Dan wasan Barcelona Ronaldo de Assis Moreira wanda ya fi shahara da Gaucho Ronaldinho ya na tsare yanzu haka a kasar Paraguay.

Jami’an tsaron kasar Paraguay sun kama Tauraron ne dauke da takardun fasfo na bogi. A dalilin wannan aka gurfanar da shi a gaban wani Alkali a makon jiya.

Lionel Messi ya fara yunkurin daukar hayar manyan Lauyoyi da za su tsayawa tsohon Kyaftin din na sa wanda su ka yi kwallo tare a kungiyar Barcelona ta Sifen.

Rahotannin da mu ke samu daga Jaridar Caughtoffside sun bayyana cewa a shirye ‘Dan wasan na Argentina ya ke da ya biya Lauyoyi har Euro fam miliyan hudu.

KU KARANTA: Fasfon bogi ya sa Ronaldinho ya fada hannun ‘Yan Sandan Paraguay.

Messi zai dauki hayar Lauyoyi, ya biyasu Miliyan €4 su fito da Ronaldinho
Ronaldinho ya yi kwallo da Lionel Messi a lokacin ya na Matashi
Asali: Twitter

Idan aka yi lissafin wannan kudi a Nairan Najeriya, sun haura Naira Biliyan 1.6. A kasuwar canjin yau Ranar Alhamis, wannan kudi sun kai Naira 1,647, 000, 000.29.

Tsohon ‘Dan wasa Gaucho Ronaldinho ya na cikin wadanda su ka taimakawa Lionel Messi a Barcelona a lokacin da ya ke Matashin ‘Dan kwallo mai tasowa.

A lokacin da Ronaldinho ya bar Barcelona, Messi ya na da ‘Dan shekara 20 ne rak a Duniya. Shekaru 12 bayan wannan lokaci, tauraruwarsa ta game Duniya.

Ko da Ronaldinho wanda yanzu rayuwarsa ta ke cikin matsala ya taba samun kyautar Ballon D’or sau biyu, Yaronsa a wancan lokaci, Messi ya lashe kyautar sau shida.

Idan dai wannan labari ya tabbata, Messi ya nuna halacci ga wanda ya taimakesa a rayuwa. Har yanzu kotu ta ki amincewa da rokon Ronaldinho na tsare sa a daki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel