Gwamnati ta yi mugun ganganci na tunbuke Sanusi II – Inji Peter Obi

Gwamnati ta yi mugun ganganci na tunbuke Sanusi II – Inji Peter Obi

Mista Peter Obi wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne, ya yi Allah-wadai da tsige Muhammadu Sanusi II da aka yi daga kan sarautar kasar Kano.

Peter Obi wanda ya yi takarar mataimakin shugaban kasa a 2019 ya bayyana cewa illar tsige Sarkin yi ta fi tasiri a kan Najeriya a kan shi Muhammadu Sanusi II.

A na sa ra’ayin, tunbuke Malam Muhammadu Sanusi II ya jawowa Najeriya mummunan hadari fiye da illar da ya kamata a ce tsigewar ta yi wa tsohon Sarkin na Kano.

Tsohon gwamnan ya yi wannan jawabi ne a shafinsa na Tuwita a Ranar Laraba, 11 ga Watan Maris. Obi ya kira wannan mataki da aikin gangancin gwamnati.

“Wannan ganganci da gwamnati ta yi a jihar Kano ya tabbatar da tsoron da Masu zuba hannun jari su ke ji na shigowa Najeriya saboda rashin tsaro da bin doka.”

KU KARANTA: Aminu Ado Bayero ya fashe da kuka bayan ya zama Sarkin Kano

“A makonnin baya, a wajen wani taro a Landan, ‘Yan kasuwan kasashen Duniya sun bayyana cewa rashin doka da rashin tsaro ne babban ciwon kansu a Najeriya.”

Jagoran jam’iyyar hamayyar ta PDP ya kara da cewa: “Wannan ganganci da masu zartarwa su ka yi a Kano ya gaskata tsoron da ‘yan kasuwar kasashen waje su ke yi.”

Fitaccen ‘Dan siyasar na Kudancin Najeriya ya kuma kara da cewa: “Dole mu fi haka, mu yi abin da ya dace, idan har mu na da niyyar taka rawar gani a Duniya.”

A daidai wannan lokaci, jam’iyyar PDP ta fito ta soki wannan mataki da gwamnatin Kano ta Abadullahi Umar Ganduje ta dauka a Ranar 9 ga Watan Maris.

Fitaccen Lauyan nan mai kare hakkin jama’a, Femi Falana SAN, ya tofa albarkacin bakinsa a Ranar Talata, ya ce tsige Sanusi II ya sabawa kundin tsarin mulki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel