Kashim Shettima ya yi tsokaci a kaikaice kan batun sauke Sarkin Kano
Bayan an tunbuke Malam Muhammadu Sanusi II daga kan karagar mulkin Kano, Sanata Kashim Shettima, ya fito gaban Duniya ya yi wata magana a kaikaice.
Tsohon gwamnan na jihar Borno, Kashim Shettima, ya wallafa wani hoto a shafinsa na Tuwita mai dauke da wata magana da Winston Churchill ya taba yi.
Marigayi Winston Churchill ya taba wata magana ya na gargadin masu sakin baki su yi magana, inda ya nuna cewa hakan na iya jefasu cikin matsala daga baya.
Sanannen abin da Churchill ya fada shi ne: “Babu wanda zai iya kama ka a kan abin da ba ka fada ba, amma muddin ka bude baki, zancen ka zai iya daure ka."
Abin da hakan ya ke nufi shi ne Kashim Shettima mai wakiltar Borno ta tsakiya a majalisar dattawa ya nanata maganar da ake yi na cewa baki ke yanka wuya.
KU KARANTA: Sanusi II a jirgin ‘Yan Sanda lokacin da za a tura sa gudun hijira
Shararren ‘Dan siyasar nan kuma tsohon Firayim Ministan kasar Ingila, Winston Leonard Spencer-Churchill ya na cikin masu ra’ayin cewa baki ne ke yanka wuya.
Shettima ya yi wannan magana ne a Ranar Talata, 10 ga Watan Maris, jim kadan bayan gwamnatin Kano ta tsige Muhammadu Sanusi II daga kujerar Sarkin Birni.
Irin su Farfesa Umar Labdo su na ganin cewa yawan maganar da Muhammadu Sanusi II ya ke yi ya na cikin abin da ya jawo masa matsala da gwamnatin jihar Kano ta APC.
Shettima ya na cikin wadanda su ka yi kokarin sasanta gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da kuma tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II, amma hakan ya ci tura a 2019.
A shafin Tuwita, Sanatan ya kuma yada wani sako da ta wata ta aikawa ‘yan siyasa inda ta nuna hoton kabarin wani tsohon gwamnan Kano da ya taba barazanar tsige Sarki.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng