Bello El-Rufai ya yi magana bayan Gwamnatin Kano ta tsige Sanusi II

Bello El-Rufai ya yi magana bayan Gwamnatin Kano ta tsige Sanusi II

Jama’a su na cigaba da tofa albarkacin bakinsu tun bayan da gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa ta sauke Malam Muhammadu Sanusi daga kujerar sarautar birni.

Daga cikin wadanda su ka fito su ka yi magana jim kadan da faruwar wannan abu akwai Bello El-Rufai, wanda shi ne babban ‘Dan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Bello El-Rufai wanda yanzu haka ya ke aiki a matsayin Hadimin Sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawa watau Uba Sani, ya nuna takaicinsa kan wannan lamari.

Malam El-Rufai ya fara da cewa: “Arewa ta dade a cikin duhu, kai har gobe a cikin duhun ta ke, sakamakon munanan duk wasu alkaluma da ke nuna cigaban al’umma.”

“Mummunan labarin da ke fitowa daga Kano ya sake jefa mu cikin duhu. Duk wani Mai tunani a Arewa ya na alhinin wannan rana, muddin bai nuna ra’ayin siyasa ba.”

KU KARANTA: 'Diyar Gwamna Ganduje ta yi magana game da sauke Sanusi II

Wannan Matashi ya nuna cewa labarin tunbuke Malam Muhammadu Sanusi II daga sarautar gidan dabo bayan shekaru kusan shida a kan mulki ya girgizasa kwarai da gaske.

“Har yanzu abin ya na cigaba da girgiza ni. Dole ka yaba da kokarin gwamnan Kano na ayyukan azo-a gani da ya yi na more rayuwa da katafariyar cibiyar kula da cutar daji.”

“Haka zalika da yunkurin da ya fara na inganta ilmi, musamman na hana bara. Kuma babu matsalar tsaro. Amma Jihar Kano da Arewa sun rasa babban Saraki (Sanusi).”

Bello El-Rufai ya yi wannan magana ne a kan shafinsa na Tuwita a Ranar Litinin. Idan ba ku manta ba, Shehu Sani, ya soki sauke Sarkin da abin da ya kira giyan mulki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel