Ban san yaushe Muhammadu Sanusi II zai bar Loko ba – Sarki Abubakar Sabo

Ban san yaushe Muhammadu Sanusi II zai bar Loko ba – Sarki Abubakar Sabo

Jaridar VOA Hausa ta yi hira da Mai martaba Sarkin Garin Loko, Alhaji Abubakar Ahmad Sabo, domin jin ta bakinsa game da dawo da Muhammadu Sanusi II cikin kasarsa.

Alhaji Abubakar Ahmad Sabo ya nuna cewa ya ji wani iri a ransa a lokacin da ya ji labarin tsohon Sarkin Birnin Kano Muhammadu Sanusi II zai yi zaman gudun hijira a Loko.

Sai dai duk da haka Mai martaban ya bayyana cewa ya zama dole a rungumi kaddarar Ubangiji game da wannan jarrabawa da ta fadawa tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II.

Sarkin Garin Loko Abubakar Ahmad Sabo ya shaidawa ‘Yar jarida cewa Garin Loko ya yi wa mutumi irin tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II Kauye da yawa.

Mai Martaba Ahmad Sabo ya yi wannan magana ne a Ranar Litinin, 9 ga Watan Maris, cikin dare. A daidai wannan lokaci Muhammadu Sanusi II ya kamo hanyar zuwa Garin.

Idan ba ku manta ba, jirgin sama ya dauko tsohon Sarkin Birnin Kano ne daga Mahaifarsa zuwa Abuja. Daga nan kuma aka shirya motoci su dauko sa su ajiye a wannan Kauye.

KU KARANTA: Obasanjo ya rubutawa Sanusi II wasika bayan Ganduje ya tsige sa

Ban san yaushe Muhammadu Sanusi II zai bar Loko ba – Sarki Abubakar Sabo
Sarkin Loko Abubakar Sabo ya tausaya Muhammadu Sanusi II
Asali: UGC

Sarkin Loko ya na ganin cewa Muhammadu Sanusi II ba zai dade a wannan wuri ba kafin gwamnati ta canza masa wurin zama. Sai dai bai san yaushe ne za ayi hakan ba.

Game da lokacin da Sanusi zai bar Loko, Sarkin ya ce:

“A’a ya rage na gwamnati ne kuma wannan. Tun da abin ya faru, kin san dole a raba shi da wurin (fadar Kano). Amma ba zai cigaba da zama a nan (Loko) na din-din-din ba."

“Bai kamata ace irin wannan ya zauna a nan ba. Akwai wanda bai kai sa ba kamar Sarkin Gwandu, lokacin da aka ciresa, an kawo sa Garin Obi jihar Nasarawa”

Sarkin na Loko ya ce bayan wani lokaci gwamnati ta dauke Jokolo, ta maida shi Garin Kaduna. Don haka ya ke ganin ba za a iya ajiye Sanusi II a wannan Gari ya dade ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel