Ni ne Mukaddashin Shugaban APC a yanzu – Inji Mataimakin Sakatare Giadom

Ni ne Mukaddashin Shugaban APC a yanzu – Inji Mataimakin Sakatare Giadom

Mukaddashin mataimakin Sakataren jam’iyyar APC na kasa Cif Victor Giadom, ya ce har yanzu Adams Oshiomhole ya na nan a matsayin wanda kotu da dakatar.

Victor Giadom ya bayyana cewa dakatarwar da Alkali ya yi wa Adams Oshiomhole daga kujerar da ya ke kai na shugaban jam’iyya, ta na nan ta na aiki har yanzu.

Giadom ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya fitar da wani jawabi ga Manema labarai a Ranar Lahadi, 8 ga Watan Maris, 2020, ya na mai cewa ya karbe jam’iyyar.

Jawabin da Victor Giadom ya fitar, ya bayyana cewa ya karbe ragamar shugabancin jam’iyyar daga hannun Oshiomhole wanda yanzu aka hana dumfarar ofishinsa.

Bayan haka, Victor Giadom ya bada sanarwar cewa majalisar NEC za ta yi taron da ta shirya a Ranar Talata, 17 ga Watan Maris kamar dai yadda ta sanar a baya.

KU KARANTA: Buhari ya na kokarin shawo kan rikicin da ya barke a APC

Ni ne Mukaddashin Shugaban APC a yanzu – Inji Mataimakin Sakatare Giadom

Giadom ya ce shi ne sabon Shugaban Jam'iyya na rikon kwarya
Source: Twitter

Jigon jam’iyyar mai mulki ya bayyana cewa a matsayinsa na Sakataren APC na rikon-kwarya, doka ta ba shi damar shugabantar jam’iyyar a irin wannan lokaci.

Giadom ya nuna cewa shi ne babban mai rike da mukami a majalisar NWC ta Adams Oshiomhole, don haka ya ce yanzu shugabancin jam’iyyar ya koma hannunsa.

Yayin da rikicin cikin-gidan na APC ya ke kara cabewa, Mataimakin Sakataren ya fito ya yi wannan bayani a birnin tarayya Abuja inji Jaridar The Nation.

Sai dai wannan jawabi na Cif Giadom ya sake jefa APC cikin rudani bayan wasu shugabannin jam’iyyar sun fito sun nuna cewa ba za ayi wani taron NEC ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel