Shugaban kasa Buhari ya dauki matakin kawo karshen rikicin Oshiomhole a APC
Alamu na nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na kokarin ganin karshen rigimar da ake fama da ita a cikin tafiyar jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Rahotanni su na nuna mana cewa shugaban kasar ya fara sa baki a rikicin da APC ta samu kanta bayan kotu ta dakatar da Adams Oshiomhole daga shugaban jam’iyya.
Wata majiya daga Jaridar The Nation ta ce shugaba Buhari ya nada wasu mutum uku da su shiga su fita domin ganin an sasanta Oshiomhole da sauran ‘yan jam’iyyar.
Akwai yiwuwar kuma shugaban kasar ya roki shugabannin APC na kasa su bada gudumuwarsu wajen ganin an kashe wutar rigimar da ta barkewa APC mai mulki.
A cewar Majiyar, Buhari da na-kusa da shi ba su jin dadin yadda abubuwa su ke kankama a APC a daidai lokacin da ya ke kokarin jan ragamar shugabancin kasar.
KU KARANTA: Maganar sauke Oshiomhole ta sa manyan APC sun rabu - Rahotanni
Wannan rikicin cikin gida da ya aukowa APC zai iya karkatar da hankalin gwamnatin shugaba Buhari daga yin aikin da ke gabanta a yanzu, don haka ta fara daukar mataki.
Ya ce: “Shugaban kasar ya kafa wani kwamitin mutane uku da za su zauna da gwamnonin (APC) domin su janye kayan yakinsu, saboda a kai ga samu zaman lafiya a jam'yya.”
Majiyar ta kara da cewa: “Buhari ya kuma bukaci kwamitin su tabbatar sun yi wa kowa sulhu. Yanzu kwamitin ya gana da wasu fusattun Gwamnoni da manyan jam'iyya.”
“Wannan rikici ya na yi wa shugaban kasa ciwo ganin cewa ana kawar da hankalin gwamnatinsa a lokacin da ya zauna da kyau domin cigaba da wa’adinsa na biyu.”
“Shugaban kasar ya rasa gane abin da ya jefa APC cikin rikicin da ba a bukata. A na sa ran cewa za a cin ma matsaya kafin ‘Yan adawa su ribaci wannan dama." A cewarsa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare
Asali: Legit.ng