Ba na goyon bayan a tsige Adams Oshiomhole – Inji Gwamna Yahaya Bello

Ba na goyon bayan a tsige Adams Oshiomhole – Inji Gwamna Yahaya Bello

Jam’iyyar APC ta samu kanta a cikin kazamar rigimar da ta kai kotu ta dakatar da shugabanta na kasa, Adams Oshiomhole, ana zargin wasu gwamnoni da hannu a wannan rikicin.

Wani daga cikin wadannan gwamnoni, ya fito ya karyata rade-radin da ake ji na cewa ya na cikin gwamnonin da ke kokarin ganin bayan Kwamred Adams Oshiomhole a jam’iyyar APC.

Wannan ba kowa ba ne illa gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, inda ya ce sam bai da hannu a yunkurin tsige Adams Oshiomhole daga kujerar da ya ke kai na shugaban APC na kasa.

Alhaji Yahaya Bello ya yi wannan bayani ne ta bakin Kwamishinansa na yada labarai, Kingsley Fanwo. Gwamnan ya ce ba zai yi abin da zai kawo rashin zaman lafiya a Jam’iyyar ba.

Adams Oshiomhole ya zargi wasu Gwamnoni da Ministocin gwamnatin APC da cewa su ne ke neman tsige shi. Hakan ya zo daidai da abin da wasu Jiga-jigan jam’iyyar su ka fada.

KU KARANTA: Gwamnoni sun nemi Jam’iyya ta maido wadanda Oshiomhole ya kora a NWC

Ba na goyon bayan a tsige Adams Oshiomhole – Inji Gwamna Yahaya Bello

Alhaji Yahaya Bello ya ce ya na tare da Adams Oshiomhole a APC
Source: Facebook

Hilliard Eta wanda shi ne Mataimakin shugaban APC na shiyyar Kudu maso Kudu, ya lissafo gwamnan na jihar Kogi a cikin wadanda su ke kokarin ganin an tunbuke Oshiomhole.

Mai girma Kwamishina Kingsley Fanwo ya shaidawa Jaridar Daily Independent cewa Yahaya Bello ya na cikin gwamnonin da su ka sa kishi da kunar jam’iyyar APC a cikin ransu.

“Gwamna Yahaya Bello ba zai taba yin abin da zai wargaza zaman lafiya jam’iyyar APC ba. Burinsa a kullum shi ne zaman lafiya da amicin APC. Cikakken ‘Dan jam’iyya ne.”

A cewar Kwamishinan na jihar Kogi, abin da gwamnan ya ke hange ya zarce siyasar zaben 2023, zai so a cigaba da damawa da shi har bayan nan, don haka ba zai kawowa APC cikas ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel