PGF: A dawo da ‘Ya ‘Yan Jam’iyyar da aka dakatar – Gwamnonin APC

PGF: A dawo da ‘Ya ‘Yan Jam’iyyar da aka dakatar – Gwamnonin APC

Gwamnonin da ke mulki a karkashin jam’iyyar APC sun yi kira ga majalisar NEC ta sake duba matakin da uwar jam’iyya ta dauka na dakatar da wasu ‘Ya ‘yanta kwanakin baya.

Salihu Lukman wanda shi ne shugaban kungiyar PGF ta gwamnonin APC ya rubutawa jam’iyya wata takarda da nufin ta dawo da duk wasu manya da aka dakatar daga jam’iyyar.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust, wannan wasika da ta fito daga hannun Darekta Janar na kungiyar ta PGF, ta shiga hannun ‘Yan jarida a jiya Ranar Asabar.

Majalisar NWC wanda Adams Oshiomhole ya ke jagoranta ta dakatar da Sanata Lawal Shuaibu wanda shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Yankin Arewacin Najeriya.

Haka zalika majalisar ta dakatar da shugaban APC na shiyyar Arewa maso Yamma Inuwa Abdulkadir. An zargi jagoran jam’iyyar ne da laifin shiryawa APC makarkashiya.

KU KARANTA: Wasu Gwamnoni su na neman APC ta nada sabon Shugaban Jam'iyya

PGF: A dawo da ‘Ya ‘Yan Jam’iyyar da aka dakatar – Gwamnonin APC

Kungiyar Gwamnonin APC ta na so a dawo da wadanda aka kora
Source: Facebook

Sauran wadanda APC ta taba dakatarwa a karkashin Oshiomhole sun hada da tsofaffin gwamnoni Ibikunle Amosun da Rochas Okorocha, da kuma gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu.

Lukman ya nemi NEC ta bi doka wajen ladabtar da ‘Yan jam’iyya da aka samu da laifi. A dalilin haka ne ya bayyana cewa taron Ranar 17 ga Watan nan zai tabo irin wadannan batutuwa.

Shugaban kungiyar ta PGF ya ke cewa bayan batun nada Mukaddashin shugaba, ya kamata APC ta shawo karshen wannan matsala na ‘Yan jam’iyyar da majalisar NWC ta dakatar a baya.

Sai dai kuma wasu Jagororin APC sun fito su na cewa babu wani taron gaggawa da jam’iyyar za ta kira. PGF ta na dai ganin Oshiomhole ya saba doka wajen dakatar da Abokan aikinsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel