Dambarwar Adams Oshiomhole ta raba kan 'Yan Majalisa NWC a Jam’iyyar APC
A sakamakon ja-in-jar da ake yi a jam’iyyar APC mai mulki na shugabanci, mun samu labari cewa makomar Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam’iyya, ta na kasa ta na dabo.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa majalisar NWC ta masu rike da jagorancin jam’iyyar APC ta rabu gida biyu bayan kotu ta dakatar da Adams Oshiomhole daga kujerar da ya ke kai.
Wasu daga cikin majalisar NWC su na goyon bayan a kira taron gaggawa a makon gobe. A daidai wannan lokaci Sakatare da Mai magana da yawun bakin APC su na ganin ba haka ba.
Wadanda ba su goyon bayan wannan mataki na kiran taron NEC sun nuna cewa a dokar APC, shugaban jam’iyya ne kadai zai iya kiran wannan taro idan har majalisar ta bukaci hakan.
Jaridar ta bayyana cewa gwamnonin APC da ba su tare da Adams Oshiomhole ne su ke kokarin ganin an kira wannan taro wanda shugaban kasa da wasu manyan APC duk za su halarta.
KU KARANTA: Ba za mu yi wani taro a Ranar 17 ga Wata ba - APC
Wadanda su ke tare da shugaban jam’iyyar da aka dakatar, su na da ra’ayin cewa yunkurin tsige tsohon gwamnan na jihar Edo daga kujerar shugaban jam’iyya na kasa, ba zai kai labari ba.
A cewar wani wanda jirgi daya ya dauko sa da Adams Oshiomhole, gwamnan jihar Edo watau Godwin Obaseki, shi ne ya ke da hannu a kokarin tunbuke shugaban jam’iyyar daga mukaminsa.
Wannan jigo na jam’iyya ya shaidawa Jaridar cewa gwamnan da wasu tsirarru ne su ke neman ganin bayan Oshiomhole, sai dai a cewarsa, mafi yawan ‘yan jam’iyyar APC ba su tare da su.
“Sama da rabin gwamnoninmu 20 da mafi yawan ‘Yan majalisar tarayya su na tare da Oshiomhole. Wasu tsirarrun gwamnoni ne su ke ganin sun fi karfin kowa, sai sun tsige sa.”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng