Ka da ka gaji da ba Shugabanni shawara a 83 – Gwamnonin Arewa ga Obasanjo

Ka da ka gaji da ba Shugabanni shawara a 83 – Gwamnonin Arewa ga Obasanjo

Kungiyar gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya, sun taya tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 83 da haihuwa a Duniya.

Shugaban wannan kungiya kuma gwmnan jihar Filato, Simon Lalong, ya fitar da wani jawabi, ya na mai jinjinawa tsohon shugaban kasar saboda hidimar da ya ke yi.

Mai girma Simon Lalong ya yabi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin mutum mai hanken nesa da kuma kishin yi wa kasarsa ta Najeriya hidima.

Mista Lalong ya bayyana cewa kishin Obasanjo wanda ya cika shekaru 83 yau bai tsaya ga gida ba, ya ce aikin Obasanjo ya ratsa Afrika da sauran kasashen Duniya.

Gwamnan na Filato ya fitar da jawabin na sa ne ta bakin Darektansa na yada labarai da hulda da jama’a, Dr. Makut Macham, Lalong a Ranar Laraba, 4 ga Maris, 2020.

KU KARANTA: Atiku ya taya Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 83

Ka da ka gajiya wajen ba Shugabanni shawara a 83 – Gwamnonin Arewa ga Obasanjo

A yau Janar Obasanjo ya cika shekaru 83 da haihuwa
Source: Twitter

Gwamnan a madadin kungiyar gwamnonin Arewa ya ke cewa Obasanjo shugaba ne wanda ya yi wa Najeriya bakin kokarinsa a mukamai da duk daman da ya samu.

Lalong ya jinjinawa kokarin da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya yi wajen kafa mulkin farar hula da shugabanci na gari da kuma kare hakkin Bil Adama a Duniya.

Shugaban kungiyar ya roki tsohon shugaban na Najeriya da cewa ka da ya gaji wajen bada shawarwarinsa na manya ga shugabannin da ke mulkin kasar a yanzu.

Lalong yace shawarar Obasanjo za ta yi wa shugabanni amfani a daidai lokacin da Najeriya ta ke kokarin cin moriyar farar hula tare da maganin sata da rashin tsaro.

Kungiyar ta ce Obasanjo ya taka rawar gani a lokacin da ya ke ofis har zuwa bayan ya sauka daga mulkin kasar. Kungiyar ta yi masa addu’ar karin samun lafiya da basira.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel