NDLEA ta kama carbi 1,360 na alburusai a kan hanyar Bauchi zuwa Jos (Hoto)

NDLEA ta kama carbi 1,360 na alburusai a kan hanyar Bauchi zuwa Jos (Hoto)

Hukumar hana sha da yaki da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Bauchi ta yi nasarar kama carbi 1,360 na alburusai yayin faturu a kan babbar hanyar Bauchi zuwa Jos.

Shugaban sashen hulda da jama'a na NDLEA, Jonah Achema, shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya aika wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NDLEA) ranar Laraba a Abuja.

Achema ya bayyana cewa sun kama alburusan ne a cikin wata motar fasinja kirar 'Vectra' a hanyarta ta zuwa Jos, babban birnin jihar Filato.

"Yayin da muke tuhumar fasinjojin motar, wasu fasinjoji guda biyu sun amsa cewa alburusan; wadanda ke boye a cikin jakankun guda biyu a bayan motar, mallkarsu ne.

"Sun dauko wannan kaya mai guba ne daga garin Numan, jihar Adamawa, kuma zasu kai wa wasu masu saya ne a jihar Filato. Masu laifin sun gaza nuna wata shaida da ta basu damar safarar alburusan.

"Sun fadi gaskiya cewa sun dade sun dade suna cikin wannan harka ta safarar miyagun makamai," a cewarsa.

NDLEA ta kama carbi 1,360 na alburusai a kan hanyar Bauchi zuwa Jos (Hoto)

NDLEA ta kama carbi 1,360 na alburusai a kan hanyar Bauchi zuwa Jos
Source: Twitter

Mista Achema ya ce masu laifin sun tabbatar musu da cewa suna sayar da kowanne alburushi a kan farashin N500.

DUBA WANNAN: Gawarwaki ko ina: An shafe sa'o'i 5 ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram a Borno

Daya daga cikin masu laifin ya bayyana cewa, "kasuwanci ne a wurin mu. Al'amura sun yi tsanani a kasar na, hakan yasa dole mu nemi duk wata hanya da za mu ciyar da iyalinmu."

Kwamnadan NDLEA reshen jihar Bauchi, Segun Kolawole Oke, ya ce za su mika masu laifin da alburusan hannun rundunar 'yan sanda domin zurfafa bincike.

A cewarsa, "wurin da suka dauko alburusan da kuma inda zasu kai su, duk wurare ne da ke fama da rashin zaman lafiya sakamakon amfani da makamai ta hanyoyin da basu dace ba."

"A saboda haka, ba zamu dauki maganar safarar makamai da wasa ba," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel