Bagudu: Gwamnatin Kebbi za ta kawo dokar haramta barace-barace a kan titi

Bagudu: Gwamnatin Kebbi za ta kawo dokar haramta barace-barace a kan titi

Gwamnatin jihar Kebbi ta na yunkurin haramta barace-barace a kan titi da ake fama da shi. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a Yau Ranar Litinin.

Rahoton da mu ka samu ya bayyana cewa gwamnatin Atiku Abubakar Bagudu za ta duba yiwuwar kafa dokar da za ta haramta bara a kan titunan jihar Kebbi.

Mai girma gwamna Atiku Abubakar Bagudu ya bayyana wannan da kansa a wajen wani taro da kungiyar Daliban da ke karantar ilmin shari’a su ka shirya a jiya.

Wannan kungiya ta NUKELS ta Daliban jihar Kebbi da ke karatun ilmin shari’a ta yi taron ta na farko ne jiya a Garin Birnin Kebbi, inda ta gayyaci Gwamnan.

KU KARANTA: Wayar salula ta sa an kashe wani tsoho a Najeriya

Bagudu: Gwamnatin Kebbi za ta kawo dokar haramta barace-barace a kan titi
Gwamna Atiku Abubakar Bagudu zai hana bara a Jihar Kebbi
Asali: UGC

Sanata Atiku Abubakar Bagudu ya ce gwamnatinsa za ta kafa dokar da za ta hana bara, wannan doka za ta ba gwamnati damar cafke iyayen yaran da ke bara.

Idan har an kirkiro wannan doka kuma an sa mata hannu, gwamnatin Kebbi za ta samu hurumin damke Iyaye da masu kula da Yaran da aka bari su na bara.

Kebbi ta bi sahun gwamnatin jihar Kano inda mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya haramta bara da niyyar koyawa Almajirai ilmin boko na zamani.

Gwamnatin Atiku Bagudu za ta tabbatar kowane Mahaifi ko mai riko ya kula da ‘Ya ‘yansa. Wannan zai bada damar a rika lura da ‘Ya ‘ya da kyau a jihar Kebbi.

A wajen wannan taro na ‘Daliban shari’an Kebbi, Ministan shari’an Najeriya, Abubakar Malami SAN, ya yi jawabi a matsayinsa na babban Lauya daga jihar ta Kebbi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel