Babu abun da wani ya isa ya yi idan na nada dana shugaban ma’aikata - Akeredolu

Babu abun da wani ya isa ya yi idan na nada dana shugaban ma’aikata - Akeredolu

Rotimi Akeredolu, gwamnan jahar Ondo, ya ce dansa Babajide ya yi aiki tukuru a lokacin kamfen dinsa kuma cewa babu abunda kowa zai iya idan ya yanke shawarar nada shi a matsayin Shugaban ma’aikatansa.

Da yake magana a Akure a lokacin taron cin abincin dare da aka yi don bikin cikarsa shekara uku a matsayin gwamna, Akeredolu ya ce dansa ya yi kokari fiye da mafi yawancin mambobin kungiyar kamfen din.

Gwamnan na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wanda ke neman tazarce ya bukaci mutanen da su yi iya bakin kokarinsu don ganin ya samu zarcewa.

Babu abun da wani ya isa ya yi idan na nada dana shugaban ma’aikata - Akeredolu
Babu abun da wani ya isa ya yi idan na nada dana shugaban ma’aikata - Akeredolu
Asali: UGC

“Idan wani ya ce Baba (Babajide) abu kafa, kawai dariya nake yi masu. Idan Ina son na daura Baba a matsayin shugaban ma’aikatana, zai iya zama; shin kun yi kokari fiye dashi ne a kamfen din? Ku tambayi kanku, mutane nawa ne suka yi kokari fiye dashi a kamfen din? Mutane nawa?” Ya tambaya.

“Matashin na ta zuwa ko ina kuma dukkaninmu mun gan shi amma muka yanke shawarar kin aikata haka domin ba zai so ba. Dana na da wadata shiyasa, idan bai dashi, zan sa shi a wani waje, kuma babu abunda wani ya isa ya yi. Zan s shi a wajen babu abunda za ku iya yi. Ba dana bane? Ba dan jahar Ondo bane? Shin bai yi aiki ba?”

KU KARANTA KUMA: Zargin zagin gwamnan APC: An tsare Atiku Boza na PDP a kurkuku, an garkame wanda ya je belinsa

Akeredolu ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya tunkari mambobin Unity Forum, wani bangaren na jam’iyyar da ya zarga da yi masa yankan baya a kokarinsa na samun tikitin jam’iyyar a karo na biyu.

A baya mun ji cewa bayan hadin-kan da aka samu daga ‘Yan kungiyar Unity Forum na jam’iyyar APC a jihar Ondo, gwamna Rotimi Akeredolu, ya fito ya nuna cewa ba ya jin tsoron kowa.

‘Ya ‘yan jam’iyyar APC da ke karkashin lemar Unity Forum za su fito su tsaida ‘Dan takara guda daya tal wanda zai kara da Rotimi Akeredolu wajen samun tikitin APC.

Cif Bukola Adetula da Sanata Ajayi Boroffice mai wakiltar Ondo ta Arewa a majalisar dattawa sun bayyana cewa za su marawa ‘Dan takara daya baya ne a zaben gwani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel