Dangote: Kamfanin tace danyen man fetur dinmu zai shiga aiki a 2021

Dangote: Kamfanin tace danyen man fetur dinmu zai shiga aiki a 2021

Mun samu labari cewa shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce matatar man fetur din da ya ke ginawa, zai fara aiki a shekara mai zuwa ta 2021.

Aliko Dangote ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya gana da ‘Yan jarida bayan shi da wasu Jami’an gwamnatin Najeriya sun kai ziyara a wannan kamfani jiya.

Alhaji Dangote ya shaidawa jaridar Daily Trust a Ranar Asabar cewa wannan matata za ta fara aiki a badi. Sannan kuma za a fara buga takin zamani a shekarar nan.

Dangote da Manajan kamfaninsa, Olakunle Alake, da kuma gwamnan bankin CBN da mataimakiyarsa, su na cikin wadanda su ka ziyarci matatar da ke Lekki.

A cikin Watan Mayun bana, ake sa ran kamfanin na Dangote ya fara aikin hada takin zamani na ‘Urea’. Attajirin Nahiyar, Dangote ya ce za a bi wannan aiki ne daki-daki.

KU KARANTA: Dangote ya saye motocin N60b a hannun kamfanin Najeriya

Dangote: Kamfanin tace danyen man fetur dinmu zai shiga aiki a 2021
Wani bangare na matatar man da Dangote ya ke ginawa a Legas
Asali: UGC

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa da zarar matatar ta fara aiki, Najeriya za ta iya fitar da man da ake bukata a gaba daya Afrika.

Da wannan namijin aiki, Mai kudin Nahiyar Afrikan ya nunawa Najeriya cewa ba dole sai an zo daga kasashen ketare sannan za iya taimakawa tattalin arzikin Najeriya ba.

“Mu na bukatar mu godewa Aliko Dangote da wannan jajircewa ta sa da zuciyar alheri. Wannan aiki ne da ba kowa ba ne zai iya tunanin kinkimo shi.” Inji Godwin Emefiele.

Wannan matata da Dangote ya ke shirin kammalawa za ta iya tace gangar mai 650, 000 a kowace rana. Wannan zai sa Najeriya da wasu kasashen Afrika su daina shigo da mai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel