Azzaluman shuwagabanni ne suka janyo talauci a Arewacin Najeriya – Shehu Sani

Azzaluman shuwagabanni ne suka janyo talauci a Arewacin Najeriya – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani yabayyana cewa azzaluman shuwagabanni ne suka gadar ma yankin Arewacin Najeriya bakin talauci da barace barace, don haka yace yin doka kadai ba zai warkar da talauci a yankin ba.

Sanatan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, inda yace: “Barace barace a Arewa sakamako ne na talauci, zalunci, rashin kula da kuma matsalolin al’ada da addini, don haka shuwagabannin Arewa su sani babu yadda za’a yi su kawar da mabarata.

KU KARANTA: Gwamnatin Amurka ta baiwa Masallatai daman kirar Sallah ta lasifika

Azzaluman shuwagabanni ne suka janyo talauci a Arewacin Najeriya – Shehu Sani
Azzaluman shuwagabanni ne suka janyo talauci a Arewacin Najeriya – Shehu Sani
Asali: UGC

“Su kansu mabaratan azzaluman shuwagabanni ne suka jefa su cikin halin da suke ciki, don haka ba z aka iya kawo karshen bara ba, ba tare da ka kawo karshen jahilci da talauci ba, za ka iya kama mabarata, amma ba zaka iya hana bara ba idan har matsalolin da suka haifar dasu suna cigaba da wanzuwa.” Inji shi.

A wani labarin kuma, A kokarinsa na tabbatar da dokar bayar da ilimi kyauta kuma ilimi dole a jahar Kano, gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya haramta duk wani almajiri yin barace barace a kan titunan jahar.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata, 25 ga watan Feburairu yayin taron mika takardun shaidar daukar aiki ga malamai yan sa kai guda 7,500 da gwamnatin ta dauka don koyarwa a makarantun firamarin jahar.

Mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwar ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar, inda yace gwamnatin Kano ta sanya almajirai cikin dokar ilimin ne da nufin shawo kan matsalar barace barace.

“Wannan tsari na ilimi kyauta a matakin sakandari da firamari zai tafi ne tare da sanya tsarin karantar da almajirai cikin tsaron boko, hakan na nufin dole ne a sanya ilimin turanci da lissafi a jadawalin karatun almajirai.

“Yayin da zasu cigaba da karatun Qur’ani, za kuma su koyi ilimin turanci da lissafi, hakan zai basu daman cigaba da karatunsu zuwa matakin Sakandari har ma gaba da haka, sabbin malamai 7,500 zasu koyar da darussan turanci da lissafi a makarantun almajirai.” Inji sanarwar.

Don haka Ganduje ya gargadi duk wani alaramma da bai bi wannan doka ba sai dai ya fita daga jahar Kano gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel