Tubabbun 'yan Boko Haram daga Nijar sun isa Maiduguri

Tubabbun 'yan Boko Haram daga Nijar sun isa Maiduguri

Tubabbun ‘yan Boko Haram da matansu da cikin kwanakin nan suka mika makamansu ga sojoji a jamhuriyar Nijar sun isa Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

Tsoffin ‘yan ta’addan sun isa filin sauka da tashin jirage na Maiduguri ne a jirgin sojoji tare da sojojin da suka samu jagorancin Bamidele Shafa, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Shafa ya ce, “mun kawo mutane 25 da suka hada da mata da maza tare da kananan yara.”

Ya ce tubabbun ‘yan Boko din sun yada makamansu tare da mika kansu ga gwamnatin kasar Nijar wadanda suka tuntubi gwamnatin Najeriya don dawo da su gida.

Tubabbun 'yan Boko Haram daga Nijar sun isa Maiduguri
Tubabbun 'yan Boko Haram daga Nijar sun isa Maiduguri
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An bayyana dalilin da yasa 'yan kungiyar ISWAP suka kashe dan Mohammed Yusuf

“Mun dawo da su gida lafiya kuma mun mika su ga gwamnatin jihar Borno don gyara. Muna amfani da wannan damar wajen kira ga wadanda har yanzu suke daji da su fito. Su amsa kiran shugaban kasa da ya basu damar yada makamansu tare da rungumar zaman lafiya,” yace.

Kwamishinar al’amuran mata ta jihar Borno wacce ta karba tubabbun, ta ce gwamnatin jihar za ta samar musu ta tallafi, ta ciyar da tufatar da su tare da basu ilimi da kuma sana’o’in dogaro da kai.

Ta ce Gwamna Babagana Zulum ya samar da cibiya mai cike da kayan koyon sana’o’i wacce zasu yi amfani da su wajen koyon sana’ar kafin a mika su ga iyalansu da ‘yan uwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel