NWC: An kai karar Shugaban APC Adams Oshiomhole da Abiola Ajimobi a gaban kotu
Mun samu labari cewa shugaban jam’iyyar APC na Garin Ado-Ekiti, jihar Ekiti, Mista Michael Akinleye, ya kai karar uwar jam’iyya a gaban Alkalin kotu.
Michael Akinleye ya na zargin shugabannin APC da yunkurin kakaba Abiola Ajimobi a kan kujerar mataimakin shugaban APC na Kudancin Najeriya.
Michael Akinleye wanda ya ke ikirarin cewa ya na cikin masu neman kujerar mataimakin shugaban jam’iyyar APC, ya fadawa kotu an toye masa hakki.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa Akinleye ya shigar da karar ne ta hannun wasu Lauyoyi biyu da su ka tsaya masa; T. J. Omidoyin da da Tunde Oke.
A cewarsa, kokarin da Adams Oshiomhole ya ke yi na daura Sanata Abiola Ajimobi a kan wannan kujera da yanzu babu wanda ya ke kai, ya ci karo da ka’idar APC.
KU KARANTA: 'Yan takarar APC sun sha alwashin hana Gwamna Akeredolu tazarce
Jagoran na APC ya ce ya bayyana shirinsa na neman wannan kujera ne a wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar APC na Ekiti a Ranar 20 ga Junairu.
Mista Akinleye ya shaidawa kotu cewa tun tuni ya roki shugabannin APC na jihar Ekiti su tsaida shi a matsayin ‘Dan takarar matamakin shugaban jam’iyyar.
Mai karar ya gabatar da wannan wasika da ya aika a Watan jiya a matsayin shaida a karar da ya shigar. APC ta ce kotu ta kawo mata takardar wannan shari’a.
Bayan Sanata Abiola Ajimobi da Michael Akinleye, ana tunanin cewa Sanata Gbenga Aluko ya na harin kujerar, kuma shi ne ke da goyon bayan APC ta jihar Ekiti.
Wadanda ake kara sun hada da: Shugaban APC na kasa, majalisar NWC, mataimakin shugaban APC (Kudu maso Yamma), Abiola Ajiombi da wasu mutum biyar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng