Gwamnan Jihar Ondo ya ce Buhari ne silar hawansa kujerar mulki a 2016

Gwamnan Jihar Ondo ya ce Buhari ne silar hawansa kujerar mulki a 2016

Mai girma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya fadawa shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa mutane su na son ganin ya cigaba da mulki a matsayin gwamna.

Idan ba ku manta ba, hukumar zabe na kasa mai zaman kanta watau INEC, ta sa Ranar 10 ga Watan Oktoba, a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo.

Gwamna Akeredolu ya yi magana ne a Garin Ore kafin shugaban kasa ya kaddamar da wani kamfani mai suna Ondo-Linyi da kuma gadar sama da gwamnatin jihar ta gina.

Gwamnan ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin Mutum mai cika alkawari, ya kuma gode masa saboda irin taimakon da gwamnatinsa ta ke ba jihar Ondo.

Rotimi Akeredolu ya ke cewa: “Ka bamu goyon bayan zuwa nan. Ba don shugaban kasa ba, ba za mu kasance a nan ba. Saboda haka wannan duk aikin ka ne Ran ka ya dade.”

KU KARANTA: Masu neman Gwamna a APC za su hada-kai wajen takara da Akerdo

Gwamnan Jihar Ondo ya ce Buhari ne silar hawansa kujerar mulki a 2016
Gwamna Akeredolu ya ce Buhari ya na da hannu a nasararsa
Asali: Twitter

Kamar yadda Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a Ranar 25 ga Watan Fubrairun 2020, Akeredolu ya bayyana cewa ba don goyon bayan Buhari ba, da bai dare kujerar gwamna ba.

“Aikin ka (Buhari) ne ya kawo mu ofis da har mu ka yi wa jama’a abin da su ke jin dadi yanzu.”

“Mutanenmu su na so mu zarce. Kuma na tabbatarwa shugaban kasa cewa a yau, mu na cika burinmu na kafa masana’antu. Ina son gode maka da ka zo aka yi wannan da kai.”

Mista Akeredolu ya kare jawabin na sa kafin a kaddamar da kamfanin a jiya Talata da cewa: “Mun gode Mai girma shugaban kasa kuma Allah ya yi maku albarka gaba daya.”

Buhari ya isa Garin Ondo ne da kimanin karfe 12:00 na Ranar Talata. Tawagar da ta tarbi shugaban Najeriya ta kunshi gwamnonin Ogun, Edo da Ekiti da Ministoci da Sarakuna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel