Boko Haram: Majalisa ta yi magana a sakamakon ta’adin da aka yi a Garkida

Boko Haram: Majalisa ta yi magana a sakamakon ta’adin da aka yi a Garkida

Majalisar dattawan Najeriya ta ba shugaban hafsun sojin kasa, Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai, umarni ya kafa sababbin sansanin Sojojin kasa a wasu wurare.

Sanatocin sun bukaci a kafa sansani ne a Garin Garkida a jihar Adamawa da kuma duk wani Gari da ke bakin iyaka da Dajin Sambisa inda ‘Yan ta’adda su ka yi karfi a baya.

Sanata Aishatu Dahiru Ahmed mai wakiltar Yankin Adamawa ta tsakiya a majalisar dattawa ce ta kawo wannan kudiri a jiya, wanda kuma ya samu karbuwar Sanatoci.

Aishatu Dahiru Ahmed ta shaidawa zauren majalisar cewa ‘Yan ta’adda sun kai hari kwanaki a wadannan wurare wanda a sanadiyyar haka, aka jikkata mutane da-dama.

A harin da Boko Haram su ka kai a Ranar 21 ga Watan Fubrairun, sun kashe Sojoji uku, sun ruguza makarantu, da asibitoci, da kuma ofisoshin ‘Yan Sanda da na’urorin sadarwa.

KU KARANTA: Gwamnatin Ganduje ta haramta bara a Jihar Kano

Boko Haram: Majalisa ta yi magana a sakamakon ta’adin da aka yi a Garkida
Majalisa ta na so a sake gina inda Boko Haram su ka ruguza
Asali: Twitter

Sanatar ta jam’iyyar APC ta ce ‘Yan ta’addan sun shiga cikin karamar hukumar Gombi da makamai a kan babura. ‘Yan ta’addan sun kai farmaki ne a wata Ranar Juma’a.

“Harin ya na da burbushin addini inda aka rika kona coci da gidajen Bayin Allah ainihin ‘Yan Garin Garkida wanda ake zaman lafiya tare da su a Yankin da ma jihar Adamawa.”

“A sakamakon haka, ya kamata ayi maza a dauki matakin gaggawa a dalilin harin da ake kai wa sha’anin tsaro, da yankin Adamawa, da kuma fadin Najeriya.” Inji Sanatar APC.

Majalisar dattawan kasar ta kuma bukaci hukumar NEDC mai kula da cigaban yankin Arewa maso Gabas, da ta sake gina wurare da gidajen addini da Boko Haram su ka rusa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel