Ba na jin tsoron gayyar da aka yi mani a Jam’iyyar APC – Akeredolu

Ba na jin tsoron gayyar da aka yi mani a Jam’iyyar APC – Akeredolu

Bayan hadin-kan da aka samu daga ‘Yan kungiyar Unity Forum na jam’iyyar APC a jihar Ondo, gwamna Rotimi Akeredolu, ya fito ya nuna cewa ba ya jin tsoron kowa.

‘Ya ‘yan jam’iyyar APC da ke karkashin lemar Unity Forum za su fito su tsaida ‘Dan takara guda daya tal wanda zai kara da Rotimi Akeredolu wajen samun tikitin APC.

Cif Bukola Adetula da Sanata Ajayi Boroffice mai wakiltar Ondo ta Arewa a majalisar dattawa sun bayyana cewa za su marawa ‘Dan takara daya baya ne a zaben gwani.

‘Yan siyasar za su yi haka ne domin su samu damar doke gwamna Rotimi Akeredolu wajen samun tutan takarar gwamna a karkashin APC a zaben jihar na bana.

Mai girma gwamnan, ya maidawa ‘Yan siyasar martani, ya ce wannan aikin da su ke yi ba zai tada masa hankali ba. Gwmanan ya yi magana ne ta bakin Segun Ajiboye.

Segun Ajiboye wanda shi ne babban Sakataren yada labarai na gwamnatin Ondo, ya fitar da jawabi, ya ce gwamnan ba ‘Dan siyasa ba ne da ke neman mulki ido rufe.

KU KARANTA: Tsohon Jigon PDP zai shafe shekaru 39 a cikin gidan yari - Kotu

Ba na jin tsoron gayyar da aka yi mani a Jam’iyyar APC – Akeredolu
'Ya 'yan APC za su kara da Akeredolu a zaben tsaida 'Dan takara
Asali: Twitter

A cewar gwamnan, kaunar da mutanensa su ke yi masa bai canza ba, don haka ya ce taron dangin da wasu ‘Yan siyasa ke yi a cikin jam’iyyar bai razana so ko kadan.

Gwamnan ya kuma zargi wasu daga cikin Jagororin jam’iyyar APC da yunkurin kawowa jam’iyyar matsala tare da jefa Yankinsu a cikin wani hali saboda burinsu.

Mista Akerodolu ya ce duk da mugun nufin da wadannan ‘Yan siyasa su ke yi, hakarsu ba ta cin ma ruwa ba. Ya ce dokar kasa ta ba kowa dama ya nemi kujerar gwamna.

“Abin da mu ka so mu yi da farko shi ne mu yi watsi da babatun Sanata (Boroffice), domin hakan ya fi dacewa da mutumin da ya saba kitsawa mutanensa sharri.” Inji gwamnan.

“Amma kuma mutane, musamman masoyan jam’iyyar mu ta APC mai daraja, sun cancanci su san cewa surutai ne kawai Boroffice ya ke yi bayan ya fado kasa babu nauyi.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel