Yadda Gwamnatin Shugaba Buhari za ta ba Bagudu $110m daga kudin Abacha

Yadda Gwamnatin Shugaba Buhari za ta ba Bagudu $110m daga kudin Abacha

Duk da gwamnatin Muhammadu Buhari ta musanya zargin cewa ta na da niyyar ba gwamna Atiku Bagudu kaso daga cikin kudin satar Sani Abacha, akwai alamun ba haka lamarin ya ke ba.

Jaridar Premium Times ta bayyana cewa gwamnatin Buhari ta gama tsara yadda za a ba Atiku Bagudu fam Dala miliyan 100 daga cikin kudin satar da Amurka za ta dawowa Najeriya da su.

Takardun da Jaridar ta samu sun nuna cewa gwamnatin Buhari ta na kalubalantar Amurka a kan zargin wani ‘Danuwan gwamnan APC, Ibrahim Bagudu, da ta ke yi da hannu a badakalar kudin.

Haka zalika gwamnatin tarayya ta na ta kokarin yakar yunkurin da kasar Amurka ta ke yi na bada damar a cire wannan yarjejeniya daga cikin takardun sirri, domin Duniya ta san maganar.

Wadannan takardu da su ka shigo hannun Premium Times sun nuna cewa gwamnatin shugaba Buhari ta na boye gaskiyar hanyar da ta ke bi wajen karbo dukiyar da Sani Abacha ya sace.

KU KARANTA:

Yadda Gwamnatin Shugaba Buhari za ta ba Bagudu $110m daga kudin Abacha
Za a ba Gwamnan Kebbi wasu kudi daga dukiyar da Abacha ya wuwura
Asali: Twitter

Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN, ya fadawa Duniya cewa za su bi ke-ke-da-ke wajen karbo wannan kudi, amma takardun kotun da ke kasa sun nuna cewa ba haka abin ya ke ba.

A Ranar 3 ga Watan Fubrairun 2020, Najeriya ta hannun wani, ta shigar da kara a kotu, ta na kalubalantar hukuncin da wata kotun kasar Amurka ta yi game da sirrin wannan yarjejeniya.

Amurka ta na ganin cewa bai kamata a bar wannan magana a matsayin sirri ba. Amma Lauyan da ke kare gwamnatin Najeriya, Anthony Egbase, ya nunawa kotu cewa bai yarda da hakan ba.

Haka kuma Buhari bai daukaka karar da Bagudu ya shigar a Ingila, ya na neman a ba shi $110 daga cikin kudin ba, sai ma dai ta fara kokarin tura kudin ga Gwamnan da ‘Danuwansa Ibrahim.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel